A farke ko a cikin barcina, Nigeria ce ke mun yawo a cikin kwakwalwata - Buhari

A farke ko a cikin barcina, Nigeria ce ke mun yawo a cikin kwakwalwata - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya jaddada cewa saboda kishin da yake yiwa kasarsa, walau yana a farke ko yana barci, Nigeria da 'yan Nigeria ne a cikin kwakwalwarsa

- Buhari ya ce gwamnatinsa ba ta da wasu kudade da zata iya rabawa 'yan Nigeria kyauta, amma zata ci gaba da samar da gine gine na bunkasa rayuwar jama'a

- Shugaba Buhari, ya kuma buga kirji da cewa jam'iyyar APC zata kasance mai nasara a zabuka masu zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa saboda kishin da yake yiwa kasarsa, walau yana a farke ko yana barci, Nigeria da 'yan Nigeria ne a cikin kwakwalwarsa, tare da tunanin hanyoyin da zaibi domin kawo hanyoyin saukakawa rayuwar jama'ar kasar baki daya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Litinin a yayin rufe wani taron bita kan ilimin masu kad'a kuri'a, wanda sashen tsare tsaren zabe da sa ido na jam'iyyar APC ya shirya kuma ya gudanar a Abuja.

Buhari ya ce gwamnatinsa ba ta da wasu kudade da zata iya rabawa 'yan Nigeria kyauta, amma zata ci gaba da samar da gine gine na bunkasa rayuwar jama'a da kuma ci gaba da samar da ababen more rayuwa daga manyan bangarorin da kasar ke samun kudaden shiga.

KARANTA WANNAN: Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

A farke ko a cikin barcina, Nigeria ce ke mun yawo a cikin kwakwalwata - Buhari

A farke ko a cikin barcina, Nigeria ce ke mun yawo a cikin kwakwalwata - Buhari
Source: UGC

Shugaban kasa Buhari ya jaddada cewa gwamnatin APC mai ci a kasar zata ci gaba da gina tituna, layin dogo da kuma bunkasar samar da wutar lantarki a birni da kauyuka da ke a cikin kasar.

Haka zalika ya bukaci mahalarta taron bitar da su kasance masu wayar da kan masu kad'a kuri'a akan bukatar da ke da akwai na sake zabar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.

Shugaba Buhari, wanda ya buga kirji da cewa jam'iyyar APC zata kasance mai nasara a zabuka masu zuwa, ya ce sakamakon zabukan maye gurbi da aka gudanar a wasu jihohi da suka hada da Edo, Ondo, Etikiti, Katsina da Bauchi da dai sauransu ya tabbatar da wannan zance nasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel