Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar jigo a APC, Hajiya Fati Muhammad

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar jigo a APC, Hajiya Fati Muhammad

- Allah ya yiwa jigo a jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Hajiya Fati Muhammad rasuwa

- Fati Muhammad ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta fadi yayin wani taro na jam'iyyar APC na mazabar Adamawa ta Tsakiya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan ta da abokan arziki da jam'iyyar APC baki daya

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Adamawa bisa rasuwar jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Hajiya Fati Muhammad.

Kafin rasuwar ta, marigayiya Fati Muhammad mamba ce a kwamitin amintattu na jam'iyyar APC. Kuma itace tsohuwar ma'ajin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party, ANPP.

Shugaba Buhari ya yi alhinin rashin jigo a APC, Hajiya Fati

Shugaba Buhari ya yi alhinin rashin jigo a APC, Hajiya Fati
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari ya aikata abin kunyar da ko gwamnatin soji ba za ta aikata ba - Atiku

A yayin da ya ke mika ta'aziyyarsa ga iyalan Fati da jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Shuagban kasar ya ce ya yi matukar bakin ciki game da rasuwar goggagiyar 'yar siyasar da ya ji dadin aiki ta ita na shekaru masu yawa.

A sakon da mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan fanin kafafen yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce ya yi bakin cikin samun labarin cewa Hajiya Fati ta yanke jiki ta fadi ne a yayin taron APC na mazabar Adamawa ta Tsakiya da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya hallarta, an garzaya da ita asibitin koyarwa na Yola inda aka tabbatar da cewa ta rasu.

"Jam'iyyar ta APC tayi rashin jagora mai wadda ta ke kaunar aikin ta sosai. Ina mika ta'azziya ta ga iyalan ta da abokan arzikin ta," inji shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel