Kul ku ka taba Jihar Imo – Okorocha ya gargadi Sakataren yada labaran APC

Kul ku ka taba Jihar Imo – Okorocha ya gargadi Sakataren yada labaran APC

Mun samu labari daga jaridar The Nation a yau dinnan cewa Mai girma gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yayi kira ga jam’iyyar sa ta APC mai mulki cewa ta guji ruguza shugabannin ta da ke jihar.

Kul ku ka taba Jihar Imo – Okorocha ya gargadi Sakataren yada labaran APC

Okorocha yace ‘Dan PDP Isa Onilu su ka tsaida takara a Imo
Source: UGC

Gwamna Rochas Okorocha ya gargadi Lanre Issa-Onilu wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na APC na kasa baki daya cewa ka da ya sake ya taba tsarin shugabancin jam’iyyar a jihar Imo a lokacin da ake shirin zabe.

Rochas Okorocha yace barnar da Mallam Lanre Issa-Onilu da ‘yan kanzagin sa su kayi a jam’iyyar APC ya isa haka, inda ya zargi jam’iyyar da tsaida ‘dan PDP a matsayin wanda zai yi takarar gwamna a jihar Imo a zaben 2019.

KU KARANTA: 2019: APC ta ba tsohon gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Okorocha yayi wannan bayani ta bakin babban Sakataren sa na yada labarai watau Sam Onwuemeodo. A jawabin an ji gwamnan yana jan-kunnen Lanre Issa-Onilu da na-kusa da shi su rabu da reshen jam'iyyar APC na Imo.

Yayin da aka sa rai cewa shugaba Buhari zai shigo jihar Imo domin yayi kamfe, Rochas Okorocha yace babu abin Issa-Onilu yake yi sai yada rade-radi da labaran karya na cewa gwamnan zai tada kafar baya wajen taron na APC.

Gwamnan na Imo yayi kira ga Sakataren na APC da ya daina fadawa Duniya karya daga Abuja inda har aka ji yana cewa an tunbuke Okorocha daga matsayin sa a APC na jagoran yakin neman zaben shugaban kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel