A'uzubillahi: Mumbarin kamfe ya rufta da dan takarar gwaman PDP a jihar Arewa (Bidiyo)

A'uzubillahi: Mumbarin kamfe ya rufta da dan takarar gwaman PDP a jihar Arewa (Bidiyo)

Wani faifan bidiyon da yayi ta yawo daren ranar Litinin din da ta gabata a kafafen sadarwar sada zumunta shine na dan takarar gwamnan jihar Kebbi dake a Arewa maso yamma karkashin jam'iyyar adawa ta PDP da ya rufta da su suna kamfe.

Bidiyon dai wanda yayi ta yawo kamar wutar daji an nuna dan takarar gwamnan tare da magoya bayan sa suna shirin soma kamfen din su a wani garin da ba'a ambata sunan sa ba a daya daga cikin garuruwan jihar.

A'uzubillahi: Mumbarin kamfe ya rufta da dan takarar gwaman PDP a jihar Arewa (Bidiyo)

A'uzubillahi: Mumbarin kamfe ya rufta da dan takarar gwaman PDP a jihar Arewa (Bidiyo)
Source: Twitter

Legit.ng Hausa ta samu cewa a faifan bidiyon, dan takarar yana dai dai kammala addu'o'i kamar dai yadda aka saba a siyasance kafin ibtila'in ya auka masu.

Al'umma masu anfani da kafafen sadarwar zamanin dai sun yi ta tofa albarkacin bakunan su akan lamarin inda wasu suka nuna jimamin su akan ibtila'in .

Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin, dan takarar gwamnan da ma jam'iyyar ta sa ta PDP bata fitar da wata sanarwa ba akan hakan.

Muna addu'ar Allah ya kiyaye gaba, wadanda ibtila'in ya rutsa da su kuma, Allah ya sawaka.

Ga dai bidiyon nan kamar yadda muka samu a shafin wani daga yan jihar:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel