Allah-kare-bala'i: An nemi sojoji da dama an rasa bayan sabon harin 'yan Boko Haram

Allah-kare-bala'i: An nemi sojoji da dama an rasa bayan sabon harin 'yan Boko Haram

Labarin dake iskemu a dakin mu na wallafa labarai na nuni ne da cewa yanzu haka ana zaman dardar a wasu sassan jihar Borno bayan da aka nemi wasu sojoji da fararen hula da dama aka rasa biyo bayan harin 'yan Boko Haram a ranar Litinin din da ta gabata.

Mun samu daga majiyar mu ta Daily Trust cewa ana tsoro tare da kuma kyautata zaton cewa dakarun sojojin sun bata ne a lokuta daban-daban saboda harin na 'yan ta'addan a sansanonin su dake a karamar hukumar Kala-Balge dake a jihar ta Borno.

Allah-kare-bala'i: An nemi sojoji da dama an rasa bayan sabon harin 'yan Boko Haram

Allah-kare-bala'i: An nemi sojoji da dama an rasa bayan sabon harin 'yan Boko Haram
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabbin bayanai sun bayyana game da ma'auratan da suka rabu saboda Buhari

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa wasu sojojin har ila yau da ba'a tantance yawan su ba sun bace suma a kananan hukumomin Ngala da Mafa dukkanin su a jihar ta Borno biyo bayan harin 'yan ta'addan a karshen makon da ya gabata.

Wani wanda lamarin ya auku kusa da shi da kuma ya zanta da majiyar mu wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa a dukkan wuraren da 'yan ta'addan suka kai farmaki ba su samu wata kwakkwarar turjiya daga wurin sojojin ba.

A cewar sa, a wasu wuraren ma kafin zuwan 'yan Boko Haram din tuni sun fice daga sansanonin nasu domin neman mafaka a wasu wuraren kamar Ngala.

Haka zalika sakamakon hare-haren na 'yan ta'addan, majiyar ta mu ta tabbatar da cewa wasu fararen hula da dama sun bazama cikin daji domin tsira da ran su kuma har yanzu basu dawo ba a garuruwa da kuma kauyukan dake makwaftaka da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel