Jam’iyyar AA tana goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari a zaben 2019

Jam’iyyar AA tana goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari a zaben 2019

- Jam’iyyar adawa ta AA tace za ta goyi bayan Buhari a zaben da za ayi bana

- Action Alliance tace ‘Dan takarar APC watau Shugaba Buhari za tayi a 2019

- Ita dai APC ta bakin Issa-Onilu tace babu abin da ya hada ta da Jam'iyyar AA

Jam’iyyar AA tana goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari a zaben 2019

Shugaban Jam’iyyar AA yace Buhari za su zaba ba Atiku ba
Source: Depositphotos

Yayin da bai fi saura kwanaki 18 rak a fara gudanar da babban zaben Najeriya ba, mun samu labari cewa jam’iyyar adawar nan ta AA watau Action Alliance ta kuma bayyana cewa za ta marawa ‘dan takarar APC baya ne a zaben na 2019.

Shugaban jam’iyyar AA na kasa, Kenneth Udeze, ya fito ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ne ‘dan takarar su a zaben da za ayi a watan gobe. Jam’iyyar AA ce ta tsaida surukin gwamna Okorocha a matsayin ‘dan takara a Imo.

A jiya ne Kenneth Udeze ya tabbatar da cewa mutanen sa shugaban kasa Buhari za su zaba ba Atiku Abubakar ba. Wannan abu ya ba jama’a mamaki ganin yadda APC ta nesanta kan ta daga Jam’iyyar adawar ta AA kwanakin baya.

KU KARANTA: Wata Jam'iyyar adawa ta goyi bayan takarar Buhari a zaben 2019

Udeze yayi wannan jawabi ne lokacin yaki neman zaben ‘dan takarar gwamnan ta a jihar Imo watau Uche Nwosu. An kaddamar da yakin neman zaben ne a filin wasan kwallon kafa na Dan Anyian da ke cikin garin Owerri a Imo.

Wannan sanarwa na shugaban AA ta zo ne jim kadan bayan an ji cewa za su bi Atiku Abubakar a zaben bana. Yanzu dai jam’iyyar tace za ta bi bayan Buhari ne saboda shi ya fi cancanta. APC kuwa dai tace babu ruwan ta da jam’iyyar.

A cikin ‘yan makonnin nan ne dai jam’iyyar ACPN da kuma PDM wanda ake tunani tana da kusanci da Atiku Abubakar ta daba masa wuka a wuya inda duk su ka nuna cewa su na tare da shugaba Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel