Yan bindiga sun yi awon gaba da katuwar mota sukutum, tare da fasinjoji 14 a Najeriya

Yan bindiga sun yi awon gaba da katuwar mota sukutum, tare da fasinjoji 14 a Najeriya

Wasu gungun yan bindiga dadi sun yi garkuwa da wata babbar motar bas mai cin mutane goma sha hudu a jahar Ribas bayan sun bindige direbanta har lahira, tare da wasu fasinjoji guda biyu da kwanansu ya kare, a jahar Ribas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne a yankin Rumuekpe, dake karamar hukumar Emohua ta jahar Ribas, inda yan bindigan suka tare motar yayin da take kan hanya daga garin Elele zuwa Ndele.

KU KARANTA: Kaico! Yan bindiga dadi sun bindige Fulani makiyaya 2 a Katsina, sun yi awon gaba da yaro

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewar miyagun mutane sun dade suna addabar matafiya akan wannan hanyar, haka zalika suna takura ma al’ummomin dake rayuwa a kauyukan dake makwabtaka da hanyar.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda yace yan bindigan sun tare hanya ne a daidai lokacin da suka hangi motar bas din tana karatowa, inda nan take suka bude ma motar wuta a dalilin haka suka kashe direban motar da fasinjoji biyu.

Daga nan ne kuma sai suka karkatar da kotar zuwa cikin daji, inda suka umarci sauran fasinjojin da kwanansu ke gaba dasu sauka daga motar daya bayan daya, sa’annan suka kara lulawa dasu cikin kungurmin daji.

Da aka tuntuni rundunar Yansandan jahar Ribas domin jin ta bakinsu, kaakakin rundunar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai yace a yanzu haka jami’an rundunar sun bazama farautar yan bindigan a cikin dajin don ganin sun ceto fasinjojin duka.

Daga karshe kaakakin Yansandan yace tuni suka mika gawarwakin mutane uku da suka mutu a sakamakon harbe harben yan bindigan zuwa dakin ajiyan gawa dake wani babban asibiti a kusa da yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel