Sanatocin APC da yan takaran Sanata sun ziyarci Buhari a fadar Villa

Sanatocin APC da yan takaran Sanata sun ziyarci Buhari a fadar Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin kafatanin Sanatocin Najeriya da suka fito daga jam’iyyar APC, tare da sauran halastattun yan takarar Sanata a inuwar jam’iyyar APC a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan ziyara shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya ma Sanatocin liyafar cin abincin dare, sa’annan ya tattauna dasu game da makomar jam’iyyar APC, musamman game a zaben dake karatowa.

KU KARANTA: Badakalar tallafin mai: Abokin Dangote ya bayyana yadda ya yi ma Faruk Lawan shigo shigo ba zurfi

Da yake jawabi a bayan taron, shugaba jam’iyyar APC, kwamared Aliyu Adams Oshiomole ya bayyana ma manema labaru cewa an samu nasara a wannan taro, domin komai ya tafi yadda ya kamata, a cewarsa.

Oshiomole yace taron ya bawa shugaban kasa Buhari damar ganawa da kafatanin Sanatocin jam’iyyar APC dake majalisar dattawa, da kuma yan takarar Sanata a karkashin inuwar jam’iyyar APC da yake sa ran zasu samu nasara a zaben 2019.

Bugu da kari, Oshiomole yayi fatan yan Najeriya zasu zabi Sanatocin APC ta yadda zasu samu rinjaye mai karfi a majalisar dattawan Najeriya, da ma majalisar wakilai a karkashin tsarin ‘kowanni mutum kuri’a daya.’

“Makasudin kiran taron shine don baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari daman tattaunawa da Sanatocin APC da sauran yan takarar Sanata, manufar taron shine tsara yadda jam’iyyar za ta tinkari zaben 2019 cikin sauki da samun nasara.

“Haka zalika taron ya kasance wata dama ga wasu daga cikin takaran Sanata suka yi ido hudu da shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na farko a rayuwarsu.” Inji shi.

Shima a jawabinsa, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa ko kadan bai dace ba ace majalisar dattawa ta kira zaman gaggawa akan batun sallamar tsohon Alkalin Alkalai, Walter Onnghen da shugaba Buhari ya yi ba.

Sanata Ahmad yace hakan bai dace bane sakamakon akwai shari’u da dama da aka shigar gaban kotuna daban daban akan lamarin dake goyon bayan sallamar ko rashin amincewa da matakin, don haka ba hurumin majalisa bane ta dauki mataki akan lamarin dake gaban kotu ba.

Daga karshe Ahmad Lawan ya tabbatar da cewa majalisar za ta koma bakin aiki a ranar 19 ga watan Feburairu domin tattaunawa tare da tafka muhawara game da kasafin kudin shekarar 2019 da Buhari ya mika mata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel