Onnoghen: Tsohon Shugaban Lauyoyin Najeriya ya kai korafi zuwa gaban NJC

Onnoghen: Tsohon Shugaban Lauyoyin Najeriya ya kai korafi zuwa gaban NJC

- Wani babban Lauya Olisa Agbakoba yana karar gwamnatin Buhari a gaban kuliya

- Agbakoba yana ikirarin cewa nada sabon Alkalin Alkalai da aka yi ya sabawa doka

- Babban Lauyan ya kai korafi gaban NJC a kan nada İbrahim Tanko da Buhari yayi

Onnoghen: Tsohon Shugaban Lauyoyin Najeriya ya kai korafi zuwa gaban NJC

Tsohon Shugaban Lauyoyin Najeriya yana kalubalantar nada sabon CJN
Source: UGC

Babban Lauyan Najeriya, Olisa Agbakoba SAN ya kai karar gwamnatin Buhari inda yake kalubalantar dakatar da Alkalin Alkalai da shugaban kasa yayi. Lauyan yace Allan-barin wannan mataki ya sabawa doka da tsarin Najeriya.

Olisa Agbakoba ya tafi a kan cewa babu wanda ya isa ya taba babban Alkalin kasar har sai dai idan an samu goyon baya daga majalisar shari’a ta Najeriya watau NJC. A Ranar Juma’a ne dai kuwa aka dakatar da CJN Walter Onnoghen.

KU KARANTA: Lauyoyi 25 sun shigar da shugaba Buhari kotu kan dakatar da Onnoghen

Agbakoba SAN yana nema yanzu manyan Alkalan Najeriya su yi masa fashin baki game da nada İbrahim Tanko Muhammed da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a matsayin babban Alkalin Najeriya na rikon kwarya.

Agbakoba wanda ya taba rike shugaban Lauyoyi na Najeriya gaba daya, ya tunawa NJC cewa an taba samun lokacin da ta ladabtar da wani babban Alkalin jihar Abia watau Obisike Orji wanda aka nada ba tare da amincewar ta ba.

Manyan Lauyoyin Najeriya su na zargin Buhari da yi wa dokar kasa hawan kawara. Daga ciki akwai Mike Ozekhome wanda yace dakatar da Mai shari’a Walter Onnoghen bai halatta a tsarin mulki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel