Mu na cigaba da tattaunawa game da shirin janye yajin aiki – Shugaban ASUU

Mu na cigaba da tattaunawa game da shirin janye yajin aiki – Shugaban ASUU

Mun ji cewa bayan kusan watanni 3 ana abu guda, kungiyar ASUU ta fito ta bayyana yadda ta ke ciki game da shirin dawowa bakin aiki. Shugaban kungiyar Malaman jami’an na kasa ya fito yayi magana.

Farfesa Biodun Ogunyemi wanda shi ne shugaban ASUU na Najeriya kaf, ya zanta da manema labarai a jiya Litinin inda ya bayyana cewa za su gana da gwamnati. Biodun Ogunyemi yayi wannan jawabi ne jiya a Garin Legas.

Biodun Ogunyemi ya tabbatar da cewa ASUU za ta sake yin wani zama da gwamnatin tarayya a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa a makon nan inda ake kokarin cin ma matsaya domin janye dogon yajin aikin da ake tayi a kasar.

KU KARANTA: ASUU ta fadawa Malaman Jami’a su kara daramar dogon yajin aiki

Shugaban na ASUU yace kawo yanzu ‘ya ‘yan su, na cigaba da tattaunawa game da tayin da gwamnati tayin karshe da gwamnatin Najeriya tayi masu. ‘Ya ‘yan kungiyar na ASUU su na wannan tattaunawa ne yanzu a kowace jami’a.

Farfesa Ogunyemi yace da zarar sun gama tattaunawa a kowane reshe, za su duba alkawarin da gwamnati tayi a kasa domin cin ma matsaya ko da a lokacin ana cikin tsakiyar sulhu da neman samun yarjejeniya da gwamnati.

Ogunyemi yana sa rai cewa za a cin ma matsaya a ganawar da za su yi a makon nan da manyan jami’an gwamnati. Duk yadda aka yi dai ASUU za ta fadawa ‘ya ‘yan ta, wanda su kuma za su bayyanawa kungiyar na su matsaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel