Badakalar tallafin mai: Abokin Dangote ya bayyana yadda ya yi ma Faruk Lawan shigo shigo ba zurfi

Badakalar tallafin mai: Abokin Dangote ya bayyana yadda ya yi ma Faruk Lawan shigo shigo ba zurfi

Hamshakin attajirin nan dan Najeriya, kuma shugaban kamfanin Forte Oil, Femi Otedola ya bayyana a gaban kotu a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu, inda ya fallasa yadda ya shirya ma Faruk Lawan gadar zare game da bahallatsar kudin tallafin man fetir da aka yi a shekarar 2012.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Otedola yana bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen lauyan wanda ake kara Faruk, Mike Ezekhome, inda yace hukumar DSS ce ta bashi kwarin gwiwar shirya wannan tarkon rago, hatta dala 500,000 daya baiwa Faruk ma ita ta bashi.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Kotu ta kunyata Fayose, ta tabbatar da nasarar gwamna Fayemi

Badakalar tallafin mai: Abokin Dangote ya bayyana yadda ya yi ma Faruk Lawan shigo shigo ba zurfi

Lawan Otedola
Source: UGC

Idan za’a tuna a shekarar 2012 ne majalisar wakilai ta kafa kwamitin binciken badakalar kudin tallafin man fetir a karkashin jagorancin Faruk Lawan, jigo a majalisar a wancan lokaci, inda aka samu kamfanoni da dama suna karban kudin tallafin mai ba tare da sun kawo man ba.

Daga cikin kamfanonin da Faruk ya bankado akwai Zenon Oil, kamfanin Otedola, sai dai Otedola ya zargi Faruk da neman cin hancin dala miliyan uku daga wajensa kafin ya wanke kamfaninsa daga badakalar, inda shi kuma ya kai kararsa ga hukumar DSS ba tare da saninsa ba.

A jawabinsa a gaban kotu, Otedola yace dala dubu dari biyar daya baiwa Faruk kamar yadda kowa ya gani a cikin wani faifan bidiyo, wani kaso ne daga cikin dala miliyan uku da ya nema daga wajensa, kuma hukumar DSS da kanta ba shi kudin domin ta ji dadin kama Faruk da hujja.

“Hukumar DSS ta sanya na’urorin daukan hoto a dakina kafin zuwa Faruk domin su dauki hotunan lokacin da nake mika masa kudin, a yanzu haka bidiyon na hannun DSS, kuma sau biyu na bashi dala dubu dari biyu da hamsin.” Inji shi.

Sai dai lauyan Faruk ya tambayi Otedola akan menene dalilin da yasa DSS bata kama Faruk a lokacin da yake karban kudin ba, wanda hakan sai ya fi zama hujja, sai Otedola ya amsa masa da cewa bai sani ba.

Daga karshe Alkalin kotun, mai sharia Angela Otaluka ta babbar kotun tarayya dake zamanta a Apo, Abuja ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel