Yaki-dan-zamba: Rundunar Sojin Najeriya ta turawa su Shekau tsala-tsalan matan sojoji

Yaki-dan-zamba: Rundunar Sojin Najeriya ta turawa su Shekau tsala-tsalan matan sojoji

Rundunar sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force, (NAF) a turance ta ce yanzu ta tura matan sojojin saman ta ya zuwa dazukan yankin Arewa maso gabashin Najeriya dake fama da tashe-tasen hankula da masu tada kayar baya.

Zaruman matan sojojin saman, kamar yadda hafsan rundunar sojojin Air Marshall Sadique Abubakar ya ce, kwararru ne da suka san makamar aikin yaki kuma za su taimaka sosai wajen karawa dakarun dake yakin karfi.

Yaki-dan-zamba: Rundunar Sojin Najeriya ta turawa su Shekau tsala-tsalan matan sojoji

Yaki-dan-zamba: Rundunar Sojin Najeriya ta turawa su Shekau tsala-tsalan matan sojoji
Source: Facebook

KU KARANTA: Cacar baki ta kaure tsakanin Buhari da PDP

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa Air Marshall Sadique Abubakar yace rundunar da yake shugabanta ta sojin sama tana baiwa daidaito tsakanin dukkan jinsi na maza da mata muhimmanci da fifiko a cikin dukkan al'amurran su.

Haka zalika Air Marshall Sadique Abubakar ya bayyana cikakken imanin sa da cewa tabbas matan za su karfafawa sojojin su gwuiwa kuma daga karshe za su taimaka wajen kawo karshen 'yan ta'addan da suka addabi kasar.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin Najeriya a karkashin jagorancin Safsan ta, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai sun soma kera motocin sulke da na yaki manya da kanana domin fuskantar abokan gaba da sauran masu tada kayar baya a kamfanin su dake a jihar Kaduna.

Da yake bude kamfanin, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai a ranar Asabar din da ta gabata ya ce nan da shekara ta 2030, kamfanin zai soma kerawa sauran kasashen Afrika da ma duniya baki daya motocin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel