OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

- Wani bangare na kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana goyon bayan ta ga shugaba Buhari

- Sarkin Aba yace bazasu manta da biyan fansho da ababen more rayuwa da shugaban ya kai yankin ba

- Yan kasuwa sun fito kwan su da kwarkwatar su don nuna goyon bayan su

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC
Source: Facebook

Wani bangare na kololuwar kungiyar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, wacce sakataren kungiyar Mr. Uche Okwukwu ke jagoranta, ta goyi bayam cigaban mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Okwukwu da farko ya kalubalanci sanarwar farko da shugaban su Chief John Nwodo yayi akan goyon bayan PDP da kungiyar tayi.

Okwukwu ya bayyana goyon bayan ga shugaba Buhari ne a matsayin dan kungiyar Ohanaeze na gaske.

Ya sanar da goyon bayan shugaba Buhari ne a ranar talata a Aba, jihar Abia inda shugaban kasar ya kai ziyarar yakin neman zaben shi a karo na biyu.

Kamar yanda Mista Garba Shehu, babban mataimakin shugaban kasa na musamman ya fada, shugaban masarautar Aba, Mai martaba Dr Isaac Ikonne, Enyi 1 na Aba ne ya bayyana goyon bayan a karo na biyu.

Ikonne, yayi kira ga duk yan jihar Abia dasu zabi dan takarar APC.

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC
Source: UGC

Yace Kabilar Ibo, zasu cigaba da biyayya ga shugaba Buhari sakamakon biyan fansho da kuma sababbin dokoki da suka saukaka kasuwanci, wanda sarkin gargajiyar yace ya amfani inyamuran fiye da kowa.

GA WANNAN: Ashe $1m aka sacewa Mugabe a jaka yana gyangyadi bayan ya bar mulki

Ya kuma yi magana akan yawan ababen more rayuwa da cigaba da ake tayi a yankin kudu maso gabas din a matsayin dalilan da yasa suke goyon bayan shugaban.

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC

OhannaEze Ndigbo da jihar Abia sun amince da shugaba Buhari da APC
Source: Facebook

"Kuna son Najeriya kuma akwai bukatar komawar mu don yakar rashawa tare da kai Najeriya mataki na gaba. Ina so in tabbatar da cewa yan Aba da duk inyamurai zasu fito kwan su da kwarkwata don zabe," inji sarkin gargajiyar a yayin da yake daga hannun shugaban kasar.

A bangaren Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, yayi maraba da alakar dake tsakanin jihar shi da gwamnatin tarayya wanda yace hakan yazo da karuwa wacce gwamnati da mutane ke so.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya zagaya Aba yace kudu maso gabas din ta cancanci karin ababen more rayuwa.

Yayi alkawarin zai cigaba da bawa ababen more rayuwa fifiko a yankin don assasa masana'antu, aiki tukuru wanda aka san inyamuran da shi.

'Yan kasuwa a sananniyar kasuwar Ariaria sun fito kwan su da kwarkwatar su don jinjinawa shugaba Buhari wanda yaje kasuwar don kaddamar da Ariaria IPP.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel