2019: Muna bin duk wani lamari kan tsaro a Kaduna -Elrufai

2019: Muna bin duk wani lamari kan tsaro a Kaduna -Elrufai

- Gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar zai samar da tsaro yayin zabe

- Gwamnan ya sadu da shuwagabannin tsaro inda ya kai koken shi akan wasu mutane da suka sha alwashin tada husuma a lokacin ko bayan zabe

- Ya shawarci iyaye dasu ja kunnen yayayansu akan yawo da makamai lokacin zaben

2019: Muna bin duk wani lamari kan tsaro a Kaduna -Elrufai

2019: Muna bin duk wani lamari kan tsaro a Kaduna -Elrufai
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tabbatar da ya sadu da shugaban tsaro na kasar don tabbatar da zabe cikin zaman lafiya a jihar ta Kaduna.

A jawabin da yayi a taron da yayi da masu ruwa da tsaki a garin Kafanchan, Babban birnin karamar hukumar Jema'a, Gwamnan ya bayyana cewa bayanin leken asiri na kwanan nan ya nuna cewa akwai mutanen da ke da burn tada husuma a kudancin Kaduna kafin ko lokacin zabe.

Kamar yanda yace, rahoton ya nuna cewa masu shiryawan naso hatsaniyar ta watsu har zuwa sauran sassan jihar saboda sun hango faduwar su a zabe mai zuwa.

"Na sadu da shugaban tsaro Janar Abayomi Olanisakin, shugaban jami'an sojin Najeriya Lt janar Tukur Buratai da kuna sifeta janar na yan sanda Mohammed Abubakar Adamu akan zancen kuma sunyi min alkawarin karfafa tsaro a jihar Kaduna kafin da kuma lokacin zabe," gwamnan ya bayyana.

El-Rufai ya kara da cewa shuwagabannin tsaron sunce zasu turo sababbin jami'ai don dakile duk wata barazana ta tsaro.

Gwamnan ya shawarci iyaye su ja kunnen yayan su dasu zama nagari, ya kara da cewa kada su dau makamai ranar zabe.

"Ku sanar da yayayenku dasu tafi da katin zaben su na dindindin kacal zuwa gurin zabe. Yan sanda zasu kama duk Wanda suka gani da makami," yaja kunne a taron.

El-Rufai yace ya sadu da sarakunan gargajiya na kudancin Kaduna jiya don kara jaddada jan kunnen.

GA WANNAN:Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

Gwamnan ya hori mutanen jihar Kaduna dasu fito kwan su da kwarkwatar su don zaben dan takarar da suke so sannan kuma za a samar da isashen tsaro a ranar zaben.

Kamar yanda gwamnan ya fada zabe ana yi ne don saka kuria ga jam'iyya ko dan takarar da mutum ke ra'ayi don haka ba zaa samu wata matsala da hakan ba.

"Amma akwai mutanen da ke karo bambancin yare ko addini. Duk da ababen alkhairi da gwamnatin tayi wa yan kudancin Kaduna amma sun alkawarin bazasu zabe mu ba saboda jam'iyyarmu zata musuluntar da Najeriya," inji shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel