Wasu ‘yan siyasar na shirin rattaba sakamakon zabuka a wasu jihohin INEC ta hango

Wasu ‘yan siyasar na shirin rattaba sakamakon zabuka a wasu jihohin INEC ta hango

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta ankarar da cewa wasu yan siyasa na shirya yanda zasu rubuta sakamakon zabe a Otal a jihar Akwa- Ibom

- Kamata yayi su nema kuri'a daga mutane ba shirin magudi ba

- Kwamishinan zaben jihar yayi alkawarin tabbatar da zabe mai yanci da inganci

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: Depositphotos

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ankarar da cewa wasu yan siyasar jihar Akwa- Ibom na shirya yanda zasu rubuta sakamakon zabe mai zuwa a Otal, a maimakon samun kuri'u daga masu zabe.Hukumar zabe mai zaman kanta ta ankarar da cewa wasu yan siyasar jihar Akwa- Ibom na shirya yanda zasu rubuta sakamakon zabe mai zuwa a Otal, a maimakon samun kuri'u daga masu zabe.

Kwamishinan zabe na jihar, Mike Igini, ya bayyana zargin ne a jiya a wani taro da mutane don bayyana musu shirye shiryen akan zaben mai zuwa a jihar.

Igini, daya daga cikin baki mai jawabi a taron, yace, "Akwa- Ibom na daya daga cikin jihohin da basa zaben gaskiya a baya."

Ma'aikacin hukumar zaben mai zaman kanta yace, "Zan iya tabbatar muku da cewa yan siyasa a nan so suke su rubuta sakamakon zabe a otal, suna tsoron zabe."

Igini yace "A 2011, duk mugayen mutane na gudowa daga Bayelsa da sauran jihohi zuwa Akwa Ibom lokacin zabe."

GA WANNAN: Duk da asarar biliyoyin daloli da yayi karkashin mulkin APC, jiya Buhari ya burge Dangote

Yayin maganar yace Najeriya ta fadi dangane da zaben kananan hukumomi, kwamishinan zaben yayi alkawarin tabbatar muku da ingantaccen zabe a jihar Akwa Ibom. Yayin maganar yace Najeriya ta fadi dangane da zaben kananan hukumomi, kwamishinan zaben yayi alkawarin tabbatar muku da ingantaccen zabe a jihar Akwa Ibom.

A kalaman shi yake cewa: " Mun fadi warwas a zaben kananan hukumomi. Tabbas mun San ba zabe ake ba a kananan hukumomi. Shiyasa ake samun jam'iyyun dake shugabanci ke lashe zaben kananan hukumomi dari bisa dari."

"Bari in sanar daku, babu zaben da mutane ke iya magudi ba tare da hada kai da hukumar zabe ba. Babu takardar kada kuri'a da za a kaita gida don rubuta sakamako. Babu ikon jiha ko tarayya. Ikon mutane kawai zai yi tasiri a jihar nan."

A yayin da aka tambaye shi ko zai sassauta idan ya samu umarni daga sama, Igini ya amsa da,"Daga ofishin koli wato shugaban kasa sun san cewa ina biyayya ne ga kundin tsarin mulki kadai. Na gudanar da zabubbuka da dama kuma sun san abinda zan iya."

Taron ya samu halartar kungiyoyin gwamnati 20 da kuma masu lura da zabe 31 daga kananan hukumomin Akwa Ibom. Sauran bakin sun hada da wakilin NSCDC da yan sanda na jihar Akwa Ibom.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel