Onnoghen: Kasar mu bata karkashin mulkin mallakar Ingila - Oshiomhole ga Duniya

Onnoghen: Kasar mu bata karkashin mulkin mallakar Ingila - Oshiomhole ga Duniya

- Najeriya ba kungiya bace, inji Oshiomhole

- Bama bukatar shishshigi akan al'amuran cikin gida inji Oshiomhole

- A duniya ana korar masu shari'a matukar aka kama su da laifin rashawa

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Source: UGC

Shugaban Jam'iyyar APC, Adam Oshiomhole ya kushe takardar da gwamnatin US da UK da kuma yan kungiyar EU akan dakatar da alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Walter Onnoghen.Shugaban Jam'iyyar APC, Adam Oshiomhole ya kushe takardar da gwamnatin US da UK da kuma yan kungiyar EU akan dakatar da alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Walter Onnoghen.

Oshiomhole ya kushe maganar a fadar shugaban kasa bayan taron Sanatocin APC da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Najeriya ba kungiya bace. Ba za mu lamunci shishshigi ba in daga gatsali a harkokin cikin gidanmu daga kasashen waje," inji shi.

Yace a turai da US ana korar masu shari'a ba tare da ansa musu baki ba.

"Ana korar masu shari'a a fadin duniya matukar aka kama su da laifin rashawa kuma basu da hurumin kwatanta Najeriya da kasa mai cike da rashawa bayan an kori alkali mai karbar rashawa, mutane kuma suna son shiga."

GA WANNAN: Mu taru mu kori shugaba Buhari a watan Mayu - Olu Falae

Ana tsaka da guguwar dakatarwar ne UK,US da EU a takardu daban daban suka ce sun damu da cigaban.

Tuni fadar shugaban kasa ta kalubalanci maganganun su tare da cewa gwamnati bazata amince da shishshigi ba, matsayar da Oshiomhole ya kare a ranar litinin.

Bayan ganin laifin maganar, Oshiomhole yayi kira ga yan Najeriya dasu kare yancin kasar su.

"Ina tunanin yakamata muyi taka tsan tsan. Kuma mu kare yancin kasar mu," inji shi.

Duk da kalubalantar su da sukayi, yace Najeriya zata cigaba da huldar ta mai kyau da sauran kashe.

"Muna maraba da hadin guiwa da taimakon sa'o'i. Muna maraba da mutane da suke da ra'ayin tattaunawa damu idan bukatar hakan ta taso. Hakan zai gina mu kuma zai kawo cigaba a harkokin zaben mu. Wadannan sune gudumawa masu amfani da muka fi bukata," cewar Oshiomhole.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel