Jonathan ya yabawa Gwamna Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya

Jonathan ya yabawa Gwamna Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya

- Tsohon shugaban kasa Goodluck ya taya murna ga Gwamna Dickson yayin da ya cika shekaru 53 a duniya

- Ya yabawa kwazo da bajintar gwamnan a bisa kujerar jagoranci wajen inganta jin dadin al'ummar jihar Bayelsa

- Dakta Jonathan ya roki Mai Duka da ya ja kwanan Gwamna Dickson tare da ba shi kariya wajen sauke nauyin da rataya a wuyan sa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya taya murna ga gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya.

Cikin wata sanarwa da sa hannun hadimin tsohon shugaban kasa kan hulda da manema labarai, Ikechukwu a yau Litinin ya bayyana cewa, Gwamna Dickson ya ci gaba da kasancewa cikin mafi kyawun sahun gwamnonin Najeriya da suka ciri tuta ta inganta jin dadin al'ummar su.

Jonathan ya yabawa Gwamna Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya

Jonathan ya yabawa Gwamna Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban kasar ya kuma mika kokon barar sa na neman Mai Duka ya shimfida kariyar sa ga gwamna Dickson domin ya dawwama wajen bayar da gudunmuwa da taka muhimmiyar rawar gani a fannin ci gaban kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Harin mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan manoma 4 a Borno

Da ya ke zayyana jawaban sa, Dakta Jonathan ya yi tarayya da iyalai da kuma abokanan arziki wajen taya murna ga Gwamna Dickson yayin da ya cimma shekaru 53 a doron kasa.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sarakunan gargajiya na Najeriya sun gudanar da wani muhimmin taro a garin Abuja domin tumke damarar su ta tabbatar da tsarkakar gaskiya da adalci yayin babban zaben kasa na bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel