'Yan bindiga sun sace amarya da ango da wasu mutum hudu a Kaduna

'Yan bindiga sun sace amarya da ango da wasu mutum hudu a Kaduna

An shiga rudani a karamar hukumar Chukun na Jihar Kaduna bayan wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun sace wani ango da amaryarsa da kuma wasu miutane hudu a gidajensu da ke kauyen Tudun Kawo a garin.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan ango da amaryar, Yasibu da Ubaida yayin da sauran mutane hudun kuma sun hada da wani limamin mai suna Yunusa, sai wani manomi, Sarkin Noma Ya'u da kuma Malam Khalidiu da Malam Abbdullahi.

Babban kwamandan 'yan kato da gora na unguwar, Hussaini Uduwa ya tabbatarwa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin inda ya ce kauyen yana da iyaka da karamar hukumar Birnin Gwari da yayi kaurin suna wurin satar mutane.

'Yan bindiga sun sace amarya da ango da wasu mutum hudu a Kaduna

'Yan bindiga sun sace amarya da ango da wasu mutum hudu a Kaduna
Source: Twitter

Ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis yayin da 'yan bindigan suka kawo hari kauyen dauke da makamai kuma suka wuce gidan ma'auratan su kayi awon gaba da su.

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

"Kwanan su uku da daura aure wannan abin ya faru. Bayan sun sace ma'auratan, yan bindigan kuma sun sace wasu mutane hudu ciki har da limami, Yunusa da manomi, Sarkin Noma Ya'u.

"Yanzu na ke dawowa daga kauyen inda na je yiwa iyayensu jaje. Na ji iyalansu suna magana da 'yan bindigan kan yadda za a samu a biya kudin fansa a sake su," inji shi.

Ya ce an kai kara zuwa ofishin 'yan sanda da ke Buruku.

A wani labarin kuma, masu garkuwa da mutane sun sace tsohon mataimakin karamar hukumar Chikun, Nuhu Kuriga a kan hanyar Buruku zuwa Udaw a ranar Lahadi.

Da aka tuntube shi domin samun karin bayani, Mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, Yakubu Sabo ya ce zai yi bincike kafin ya bayar da bayani a lokacin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel