Harin mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan manoma 4 a Borno

Harin mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan manoma 4 a Borno

- Mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Molai a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya

- 'Yan ta'adda sun salwantar da rayukan manoma hudu a garin Maiduguri

- Dakarun kungiyar sa kai sun bayyana yadda mayakan Boko Haram suka yiwa manoma hudu yankan ragon a kauyen Molai

Wani sabon harin mayaka na Boko Haram a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, ya salwantar da rayukan wasu manoma hudu kamar yadda 'yan kungiyar dakarun tsaro ta sa kai da mazauna suka bayyana a yau Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin kungiyar ta'adda ta Boko Haram bisa jagoranci na reshen Abubakar Shekau ke da alhakin wannan mummunan hari da ya auku daura da kauyen Molai da ke da 'yar gajeruwar tazara da garin Maiduguri.

Harin mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan manoma 4 a Borno

Harin mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan manoma 4 a Borno
Source: Twitter

Kamar yadda kafar watsa labarai ta AFP ta ruwaito, jagoran dakarun sa kai, Ibrahim Usman, ya bayyana yadda masu ta'adar suka ribaci wata hanya ta mafi munin zalunci wajen salwantar da rayukan Manoman inda suka yi masu yanka irin na rago .

Baya ga wannan zalunci, ma su ta'adar sun yi amfani da wayar salula ta daya daga cikin manoman da suka sheke wajen bayyana sanarwa da kuma rahoton wasu Mutane biyu daban da suka yi garkuwa da su.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ta'addancin Boko Haram musamman a Arewa maso Gabashin Najeriya ya salwantar da fiye da rayukan Mutane 27,000 tun yayin da suka daura damarar tsageranci a shekarar 2009 kawowa yanzu.

KARANTA KUMA: Mahaifiya ta ce ta bani da umarnin sanya wa Mahaifi na guba cikin abinci - Dan shekara 10 ya yi fallasa a gaban Kotu

A yayin da dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da fafutikar yakar ta'addanci a yankun Arewa maso Gabas, a halin yanzu mayakan Boko Haram sun yi rauni ta yadda ba sa iya kai wani babban hari cikin birane illa iyaka kan 'yan tsirarin manoma da ke kauyuka da kuma bayan gari.

Ko shakka ba bu kauyen Molai da ke garin Maiduguri ya fuskanci barazana ta munanan hare-hare na masu ta'adda tun yayin da mayakan Boko Haram suka daura damarar ta'addanci a Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel