Hotuna: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom

Hotuna: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom

Dan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya garzaya jihar Akwa Ibom ranan Litinin, 28 ga watan Junairu, 2019 domin yakin neman zabensa.

Yayinda yake jawabi ga jama'ar da suka halarci taron, Atiku ya yiwa jihar Akwa Ibom alkawarin matatan man fetur domin inganta tattalin arzikin jihar.

Hotuna: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom

Akwa Ibom
Source: Facebook

Hotuna: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom

Hotuna: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom
Source: Facebook

Yace: "Tun shekarar 1998 nike zuwa jihar nan, suk cigaban da kuka gani a jihar nan aikin PDP ce. Zaku cigaba da samun nasara idan kuka cigaba da kasancewa PDP. Saboda haka, ina jinjinawa mutan jihar Akwa Ibom da cigaba da kasancewarku PDP."

"APC sun bayyana muku a 2015 cewa za su inganta tattalin arziki. Da suka zo, rashin tsaro a yankin Arewa maso gabas kadai take, amma a yau, abin ya yadu zuwa Arewa maso yamma da tsakiya."

"Daya daga cikin manyan manufofinmu shine garambawul. Idan muka sauya fasalin kasar nan, Akwa Ibom zata fi haka cigaba. Matatan man fetur zai zo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel