Akpabio ya yi alkawarin kawo wa Buhari kuri’u miliyan 10

Akpabio ya yi alkawarin kawo wa Buhari kuri’u miliyan 10

Tsohon Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Godswill Akpabio, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai lashe zaben Shugaban kasa duk kuwa da kokarin ganin rashin nasararsa da mambobin jam’iyyu adawa ke yi.

Akpabio wanda ya kasance Shugaban kwamitin kamfen din Shugaban kasa na jam’yyar All Progressives Congress (APC) yace zai kawo wa Shugaban kasar kuri’u miliyan 10.

Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya fadi hakan ne a ranar Asabar a garin Ibadan, babbar birnin jihar Oyo a lokacin kaddamar da kamfen din jam’iyyar a kudu maso yamma.

Yace yan Najeriya sun gano jajirtaccen shugaba a tattare da shugaba Buhari, sannan kuma ya kasance mutum mai son ganin chanji mai inganci a kasar.

Akpabio ya yi alkawarin kawo wa Buhari kuri’u miliyan 10

Akpabio ya yi alkawarin kawo wa Buhari kuri’u miliyan 10
Source: Depositphotos

Yace ya sadaukar da kansa domin tabbatar da cewa Buhari ya samu akalla kuri’u miliyan 10 daga kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Har kasa mai tsarki na je na rokar wa Buhari lafiya – Tambuwal

A wani labari na daban, mun ji labari cewa babban Limamin darikar Katolika masu bin addinin Kirista a Garin Yola a cikin jihar Adamawa watau Rabaren Stephen Mamza ya caccaki wasu malaman da ke kasar nan da barin aikin Allah.

Babban Shehi Stephen Mamza yayi hira da Jaridar Punch inda ya tabo batun zaben bana da kuma yadda wasu Malamai ke kutsa kai cikin siyasa.

Rabaren Mamza yace kwadayi ne yake sa Malamai su na shiga wajen ‘yan siyasan kasar. Shehin yace sam bai dace Malaman addini su rika bari ‘yan siyasa na amfani da su ba.

Limamin yace ya kamata ace Malaman addini su zama masu yi wa masu mulki wa’azi ne, amma sai su ka kare da yin abin kunya saboda kwadayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel