Har kasa mai tsarki na je na rokar wa Buhari lafiya – Tambuwal

Har kasa mai tsarki na je na rokar wa Buhari lafiya – Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi wasu bayanai akan dalilansa na ficewa daga jam'iyyar APC da dangantakarsa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Tambuwal ya bayyana cewa tun farko abubuwan da yasa ya bar PDP saboda rashin daidaitan lamura ne a karkashin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma yakinin da suka yin a cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo sauyi.

Yana mai cewa: “Abunda yasa muka hada karfi aka yi hada-kai a zaben 2015 muka kafa jam’iyyar APC saboda shawo kan matsaloln da ke gabanmu a matsayin yan Najeriya na sha’anin yaki rashawa, tsaro matsalolin da suka shafi tattalin arziki, matsalolin ci gaban al’umman da walwalarsu musamman matasa da mata na samar masu aikinyi.

Har kasa mai tsarki na je na rokar wa Buhari lafiya – Tambuwal

Har kasa mai tsarki na je na rokar wa Buhari lafiya – Tambuwal
Source: Facebook

"A lokacin ina jam’iyyar PDP mun sha nusar da Shugaban kasar waccan lokacin Goodluck Jonathan da ya fahimci cewar kasar ba ta tafiya daidai amma ya kasa fahimta ba wannan dalilin ne yasa muka yi hada-akai. Sai kuma gashi tafiya tayi tafiya abubuwa suka dada tabarbarewa yanayi ya kawo kowa ya san yadda ake gudanar da yaki da cin hanci da rashawa akwai gyara, kowa ya san almarin tsaro na so ya amaye kusan yankin arewacin kasar, yau mu da jihar Zamfara baka iya tafiya idan ya kai wani lokaci saboda kana tsoron kada a sace ka.

"Ba wai bamu son Goodluck bane a lokutan baya yasa muk barsa, a’a muna son gyaran kasar ne. Dama mun kyautata zaton cewa Shugaban kasar zai iya kawo sauyi ne, zai yi aiki sai gashi a cikin tafiyan mun gane cewa abubuwan basa tafiya yadda ya kamata."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Lauyoyi za su kaurace wa kotu tsawon kwanaki 2 – NBA

Akan batun dangantakarsa da shugaba Muhmmadu Buhari, Gwamna Tambuwl yace har birnin Makkah yaje ya fuskanci mahallicinsa domin roka masa lafiya.

Yace: "Har Baitul Muqaddas na je na sa goshi na a kasa, na rokan ma iyayena rahama, na rokar wa Muhammadu Buhari lafiya."

Kan batun neman kujerar mataimakin shugaban kasa a lokacin da Shugaba Buhari ke jinya a birnin Landan Tambuwal yace: "Allah, wanda raina ke hannunsa... Ban taba zuwa inda wani mahaluki na nemi mataimakin shugaban kasa ba. Ban taba rokon Allah Ya ba ni mataimakin shugaban kasa ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel