Dakatad da Walter Onnoghen: Lauyoyi 25 sun shigar da shugaba Buhari kotu

Dakatad da Walter Onnoghen: Lauyoyi 25 sun shigar da shugaba Buhari kotu

A yau Litinin, Lauyoyin Najeriya 25 sun shigar da shugaban Muhammadu Buhari babban kotun tarayya da ke zaune a birnin tarayya Abuja domin kalubalantar dakatad da shugaban Alkalai, Jastis Walter Onnoghen, da akayi ranan Juma'a.

Wannan kara ya biyo bayan shari'ar kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT wacce ta bayyana da safe cewa ta daga zama sauraron zargin da ake yiwa Walter Onnoghen har sai ila ma shaa'a LLahu.

Lauyoyin da suka shigar da karan karkashin jagorancin , Mr Johnmary Jideobi, ya gabatar da maganganu biyu gaban kotun.

Ya bukaci kotun da "Ta fassara sashe na 153(1) (i) akin layi na 21(a) da kuma sashe na 271, 291, 292 da 231 na kundin tsarin mulkin Najeriya, indan shugaban kasa na da karfin dakatad da Walter Onnoghen matsayin shugaban Alkalan Najeriya."

Bayan gabatar da jawabansu, sun bukaci kotun ta fadawa shugaba Buhari cewa ba shi da hurumi da karfin dakatad da Walter Onnoghen matsayin CJN.

KU KARANTA: Yakin Boko Haram: Gwamnati ta saki kudin sayan jirage yaki kiran "Tucano" 12

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Tanko a ranan Juma'a, 25 ga watan Junairu bayan sallamar shugaban Alkalan, Walter Onnoghen, bisa ga zargin boye wasu dukiyoyi da ya mallaka.

Da safiyar ranan Litinin, Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun dira ofishin shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, da safiyar Litinin bayan shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar ranan Juma'a. Majiya ta bayyanawa manema labarai

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel