Yanzu-yanzu: Majalisa dokokin jihar Legas na zaman da yamman nan, za su tsige gwamna Ambode

Yanzu-yanzu: Majalisa dokokin jihar Legas na zaman da yamman nan, za su tsige gwamna Ambode

Majalisar dokokin jihar Legas na cikin zama da yammacin yau Litinin, 28 ga watan Junairu, 2019 domin tsige gwamnan jihar, Akinwumi Ambode, bisa ga laifi da suka zarginshi da shi.

Mun samu wannan rahoto ne daga gidan talabijin ta TVC da ke zaune a Legas in tace: "Yan majalisa suna shirin tsige gwamna Akinwumi Ambode, suna zargin da laifuka."

Yan majalisan suna zargin gwamnan da kashe wasu kudade ba tare da sa hannun majalisar dokokin jihar ba.

Gwamna Ambode ya shiga tarkon jama'an jiharsa ne yayinda aka fara zarginsa da daukar nauyin dan takarar gwamnan PDP, Jimi Agbaje, a zaben da zai gudana a watan Maris.

KU KARANTA: Zan gina muku matatan man fetur - Atiku yayinda yaje yakin neman zaben Akwa Ibom

A baya, an yi masa barazanar tsigeshi jim kadan bayan ya sha kasa a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC inda kwamishana da ke karkashinsa, Babajide Sanwoolu, ya kashe zaben.

Wasu jigogin jam'iyyar APC sun bayyana cewa Ambode ba ji dadin sakamakon zaben fidda gwanin ba kuma ya karkatar da wasu kudade ta ma'aikatar ma'adinai domin taimakawa yakin neman zaben Jimi Agbaje na PDP.

Amma, gwamnan ya karyata dukkan wadannan rahotanni kuma ya jaddada biyayyarsa ga jam'iyyar.

Ambode ya sabawa tarihi a wannan shekara inda ya gaza kaddamar da kasafin kudin 2019 gaban majalisar kafin karwar shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel