Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta fitar da sabuwar sanarwa kan zaman da ta shirya yi gobe

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta fitar da sabuwar sanarwa kan zaman da ta shirya yi gobe

Majalisar dattawan Najeriya ta sanar da dage zaman da ta shirya yi na gaggawa a gobe Talata domin tattaunawa akan maganar korar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa Alkalin-alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen a karshen satin da ya gabata.

Sanarwar dage zaman na 'yan majalisar dattawan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Akawun majalisar Mista Nelson Ayewoh ya fitar ranar Lititin da yammaci dauke da sa hannun sa.

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta fitar da sabuwar sanarwa kan zaman da ta shirya yi gobe

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta fitar da sabuwar sanarwa kan zaman da ta shirya yi gobe
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun soma kera motocin yaki

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai a cikin sanarwar da ya fitar babu wani cikakken bayani kan musabbabin dalilin dage zaman ba.

Sai dai wani bincike da majiyar mu ta gudanar, ya bankado cewa ana zaton dalilin hakan shine domin 'yan majalisar ta dattawa su samu damar halartar zaman kotun da aka shigar da kara ana bukatar fashin baki kan hukuncin da Shugaba Buhari ya dauka na dakatar da Alkalin alkalan.

Ga dai takardar manema labarab nan da majalisar dattawan ta fitar:

Cikakken bayani kan hakan na nan tafe..

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel