Yanzu Yanzu: Lauyoyi za su kaurace wa kotu tsawon kwanaki 2 – NBA

Yanzu Yanzu: Lauyoyi za su kaurace wa kotu tsawon kwanaki 2 – NBA

Kungiyar lauyoyin Najeriya ta yanke shawarar kaurace ma kotu na tsawon kwanaki biyu domn yin zanga-zanga akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

Kungiyar ta NBA ta yanke shawarar ne a wani taron masu ruwa da tsakinta wanda aka gudanar a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu.

Yajin aikin zai fara ne daga ranar Talatam 29 ga watan Janairu sannan zai ci gaba har ranar Laraba.

Yanzu Yanzu: Lauyoyi za su kaurace wa kotu tsawon kwanaki 2 – NBA

Yanzu Yanzu: Lauyoyi za su kaurace wa kotu tsawon kwanaki 2 – NBA
Source: UGC

Mista Onneghen na fuskantar shari’a akan zargin kin bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka a kotun kula da da’ar ma’aikata ta CCT.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya dakatar da shi a ranar Juma’ar da ta gabata bisa ga wani umurni daga CCT.

Shugaban kasar ya aiwatar da umurnin kotun CCT duk da cewar kotun roko ta bukaci a dakatar da shari’an babban alkalin-alkalan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi

A halin da ake ciki, mun ji cewa Alkalin Alkalan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar a ranar Juma'a da ta gabata, Justice Walter Onnoghen ya karyata rahotanin da ke wasu kafafen watsa labarai na yanar gizo ke wallafa na cewa ya yi murabus.

Onnoghen wanda Shugaba Buhari ya maye gurbinsa da babban mai shari'a da ke biye masa a mukami a kotun koli, Mai shari'a Tanko Muhammed a matsayin mukadashinsa ya karyata jita-jitar a yau Litinin.

Sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a fanin kafafen watsa labarai, Awassam Bassey ya ce babu kanshin gaskiya a cikin labarin da wasu masu yada labaran karya suke wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel