Da duminsa: Banyi murabus ba - Alkalin Alkalai, Onnoghen

Da duminsa: Banyi murabus ba - Alkalin Alkalai, Onnoghen

Alkalin Alkalan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar a ranar Juma'a da ta gabata, Justice Walter Onnoghen ya karyata rahotanin da ke wasu kafafen watsa labarai na yanar gizo ke wallafa na cewa ya yi murabus.

Onnoghen wanda Shugaba Buhari ya maye gurbinsa da babban mai shari'a da ke biye masa a mukami a kotun koli, Mai shari'a Tanko Muhammed a matsayin mukadashinsa ya karyata jita-jitar a yau Litinin.

Sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a fanin kafafen watsa labarai, Awassam Bassey ya ce babu kanshin gaskiya a cikin labarin da wasu masu yada labaran karya suke wallafa.

Da duminsa: Banyi murabus ba - Alkalin Alkalai, Onnoghen

Da duminsa: Banyi murabus ba - Alkalin Alkalai, Onnoghen
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

"Wasu masu neman tayar da zaune tsaye suna cigaba da watsa labarin na karya. Babu kanshin gaskiya a cikin labarin. Alkalin Alkalai na kasa, Hon. Jastis Walter Samuel Nkanu Onnoghen, GCON, baiyi murabus daga mukaminsa ba," inji Bassey.

Wannan jita-jitar ya fito ne sa'o'i 24 gabanin taron gaggawa da Kwamitin Alkalan Najeriya ta kira domin tattaunawa a kan dakatar da Onnoghen da kuma nada Muhammad a matsayin mukadashinsa.

Tun a ranar Juma'a kungiyoyi da mutane daban-daban suna ta bayyana ra'ayoyinsu a kan dakatar da Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel