Yanzu Yanzu: Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi

Yanzu Yanzu: Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi

- Kungiyar kafamfanoni masu zaman kansu a ranar Litinin, 28 g watan Janairu ta bayyana cewa ta amince da mafi karancin albashi

- An bayyana wannan matsayar ne a wani taron tattaunawa da majalisar wakilai ta shirya akan dokar karancin albashi wanda shugaba Buhari ya gabatar

- A halin da ake ciki gwamnatin tarayya ta ce tun farko dama ba wai ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi banne

Kungiyar kafamfanoni masu zaman kansu a ranar Litinin, 28 g watan Janairu ta bayyana cewa ta amince da mafi karancin albashi wanda kwamitin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa suka bayar da shawara a kai.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bayyana wannan matsayar ne a wani taron tattaunawa da majalisar wakilai ta shirya akan dokar karancin albashi wanda shugaba Buhari ya gabatar a makon da ya gabata.

Yanzu Yanzu: Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi

Yanzu Yanzu: Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da N30,000 a matsayin karancin albashi
Source: UGC

A halin da ake ciki, Ministan kwadago da diban ma’aikata, yace gwamnatin Najeriy ba ta amince da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba kamar yadda ake ta hasashe.

Ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa kan dokar karancin albashi da ke gudana a Abuja.

A cewar Ngige, batun cewa gwamnati ta amince da N27,000 da N30,000 a matsayin karancin albashi duk kuskuren fahimta.

KU KARANTA KUMA: Uwargidar Namadi Sambo ta nuna bacin rai kan yadda ake tozarta Musulmai masu sanya hijab

Yace: “Ina so na warware wasu kuskurorin fahimta da aka samu. Kokawar cewar gwamnati ta amince da farashi biyu N27,000 da N30,000 ba gaskiya bane. Abunda gwamnati ta amince da shi daga majalisar Shugaban kasa shine N27,000 ga dukkanin ma’aikatan tarayyar Najeriya."

Ya kuma bayyana cewa wannan matsaya na gwamnati ba zai hana ma’aikata samun fiye da hakan daga ma’aikatansu ba, ya danganta da karfin aljihun wanda ya dauki mutum aiki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel