Hukumar EFCC ta hada karfi da FBI ta cafke wanda ya addabi jama’a da damfara

Hukumar EFCC ta hada karfi da FBI ta cafke wanda ya addabi jama’a da damfara

- Hukumar EFCC ta hada kai da FBI wajen damke wani fitinannen mai laifi

- Anthony Osaro wanda yayi kaurin suna wajen damfara ya shiga hannu

- FBI ta kasar Amurka ta taimaka wajen damke Mista Osaro mai shekaru 22

Hukumar EFCC ta hada karfi da FBI ta cafke wanda ya addabi jama’a da damfara

An damke wani 'dan damfara da ya addabi jama'a a Najeriya
Source: Facebook

Mun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta cafke wani Matashi mai suna Mista Anothony Osaro wanda ya fitina jama’a da damfara. Osaro Matashi ne mai shekaru kusan 22 a Duniya.

Ana zargin Anthony Osaro da damfarar Bayin Allah ta yanar gizo don haka EFCC ta ci azamar yin ram da shi. A wannan karo dai an yi dace ya shigo hannun, bayan hukumar ta hada kai da FBI mai gudanar da bincike a kasar Amurka.

KU KARANTA: Kotu ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

Vero Agboje wanda ita ce babbar Lauyar da ke karar wanda ake zargi watau Anthony Osaro a gaban kotu, ta bayyana cewa an yi ram da Matashin ne dauke da gafakar da yake aiki da ita wajen damfarar mutane a kan yanar gizo.

Wanda ake zargin yana namen yin sulhu yanzu da EFCC bayan ya shigo hannun jami’an binciken dumu-dumu. An kuma samu wasu kayan aiki na na’urar ASUS a cikin motar wannan mutumi, wata kirar Toyoto Camry ta zamani.

EFCC tace hukumar bincike ta kasar Amurka ta FBI ta taimaka mata wajen gudanar da bincike a kan Osaro. Anthony Osaro dai ya fadawa kotu cewa ya aikata duk laifuffukan da ake tuhumar sa da su, yana kuma neman sauki a gaban kuliya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel