Sabbin dalilai da suka sanya muka dakatar da Alkalin Alkalai - Gwamnatin tarayya

Sabbin dalilai da suka sanya muka dakatar da Alkalin Alkalai - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta sake shimfidar wasu sabbin dalilai da suka sanya ta dakatar da Alkalin Alkalai

- Gwamnatin ta sake bankado yadda dukumar dukiya ci gaba da da shige da fice cikin asusun ajiya na Alkali Walter Onnoghen

- Gwamnati ta ce tuhuma gami da zargin da ke kan Alkalin Alkalai sun sabawa dokokin hukumar shari'a ta kasa

A yayin da ake ci gaba da cecekuce da babatu kan dambarwar dakatar da Alkalin Alkalai na Najeriya, Justice Walter Onnoghen, gwamnatin tarayya ta sake zayyana wasu sabbin dalilai da suka sanya ta yanke hukuncin dakatar da babban Alkalin.

Alkali Walter Onnoghen tare da shugaban kasa Buhari

Alkali Walter Onnoghen tare da shugaban kasa Buhari
Source: UGC

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, dalilai da suka sanya ta yanke hukuncin dakatar da babban Alkalin na kasa ba su wuce laifin da ya aikata ba na sabawa dokokin hukumar shari'a kasancewar sa jigo a karkashin ta.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin ta bayyana hakan ne da sanadin Ministan Labarai da Al'adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed, da ya shaidawa manema labarai a yau Litinin cikin garin Abuja.

Ministan ya bayyana cewa, binciken gwamnatin tarayya ya bankado yadda wasu miliyoyi na kudade ke shige da fice cikin asusun ajiya mallakin Alkali Onnoghen da ba ta da masaniya kuma dalilan yadda aka samo su.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Sarakanun Gargajiya na Najeriya na ganawa kan zaben 2019

Alhaji Mohammed ya ce, laifin Alkali Onnoghen na rashin bayyana dukkanin kadarar sa da arziki da ya mallaka ya na cin karo da kundin tsarin hukumar tabbatar da da'a da yiwa dokoki da kuma shari'ar kasa biyayya. Sai dai Alkalin ya ce ya aikata hakan ne a bisa kuskure da ajizanci.

Ya kara da cewa, shawarar hukumar tabbatar da kiyaye doka da yiwa shari'ar kasar nan da'a ta yi daidai da hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zartar cikin gaggawa domin kare martabar kasar nan da kuma fidda ita kunya a bisa mizani na shari'a.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel