Buhari ya aikata abin kunyar da ko gwamnatin soji ba za ta aikata ba - Atiku

Buhari ya aikata abin kunyar da ko gwamnatin soji ba za ta aikata ba - Atiku

- Dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya soki dakatarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa Walter Onnoghen

- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce dakatar da alkalin alkalan wani tabargaza ne da ko gwamnatin kama-karya na soji ba su taba aikatawa ba

- Atiku ya ce Najeriya tana fuskantar wani babban kalubale kuma matakin da muka dauka zaiyi tasiri a akan demokradiyyar mu

Dan takarar shugabancin kasa na karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya sake zargin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da musgunawa fannin shari'a na Najeriya.

A jawabin da ya yi a wurin taron manema labarai da ya kira a Abuja, Atiku ya ce dakatar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen da Buhari ya yi kafa wani tarihi ne da ko a zaman mulkin kama karya na soja ba a taba ganin irinsa ba.

Buhari ya aikata abinda ko gwamnatin kama-karya na soji ba ta aikata ba - Atiku

Buhari ya aikata abinda ko gwamnatin kama-karya na soji ba ta aikata ba - Atiku
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yiwa jam'iyya zagon kasa: An tsige Okorocha a matsayin jagorar yakin neman zabe

An tuhumar Onnoghen ne da laifin rashin bayyana dukkan kadarorinsa amma Shugaba Buhari ya dakatar da shi a ranar Juma'an makon da ya gabata.

Mutane da dama sunyi soki dakatarwar da Buhari ya yi yayin da wasu kuma suna ganin dakatarwar ba ta sabawa doka ba duba da cewa kotun da'ar ma'aikata ne ta bayar da umurnin dakatarwar.

"Kasar mu tana cikin wani mawuyacin hali a yanzu. Yadda zamu fuskanci wannan kalubalen zaiyi babban tasiri a kan makoman demokradiyar mu wadda gwamnatin da ke mulki yanzu ta ke kokarin kawo rudanni a cikinsa saboda kin bin dokokin da ke kundin tsarin mulkin mu.

"Dukkan mu sheda ne a kan yadda aka saba umurnin kotunna da ke hakkin 'yan adam wadda hakan ya tabbatar mana cewa Janar Buharri da gwamnatinsa sun gwammace suyi son kai a maimakon biyaya da dokokin da ke kundin tsarin mulkin mu," inji Atiku.

Ya kara da cewa yana goyon bayan yaki da rashawa sai dai abin dubawa a nan shine 'ko an bi doka da oda wurin dakatar da Onnoghen kamar yadda ya ke cikin kundin tsarin mulki.'

Ya kuma ya kira da Shugaba Buhari ya guji aikata wani abu da zai kawo cikas ga babban zabe da ke tafe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel