Yanzu Yanzu: Gwamnatin Najeriya ba ta taba amincewa da N30,000 a matsayin karancin albashi ba - Ngige

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Najeriya ba ta taba amincewa da N30,000 a matsayin karancin albashi ba - Ngige

- Ministan kwadago da diban ma’aikata, yace gwamnatin Najeriy ba ta amince da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba tun farko

- Ngige yace batun wai gwamnati ta amince da N27,000 da N30,000 a matsayin karancin albashi duk kuskuren fahimta

- Ya kuma bayyana cewa wannan matsaya na gwamnati ba zai hana ma’aikata samun fiye da hakan daga ma’aikatansu ba, ya danganta da karfin aljihun wanda ya dauki mutum aiki

Ministan kwadago da diban ma’aikata, yace gwamnatin Najeriy ba ta amince da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba kamar yadda ake ta hasashe.

Ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa kan dokar karancin albashi da ke gudana a Abuja.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Najeriya ba ta taba amincewa da N30,000 a matsayin karancin albashi ba - Ngige

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Najeriya ba ta taba amincewa da N30,000 a matsayin karancin albashi ba - Ngige
Source: UGC

A cewar Ngige, batun cewa gwamnati ta amince da N27,000 da N30,000 a matsayin karancin albashi duk kuskuren fahimta.

Yace: “ Ina so na warware wasu kuskurorin fahimta da aka samu. Kokawar cewar gwamnati ta amince da farashi biyu N27,000 da N30,000 ba gaskiya bane. Abunda gwamnati ta amince da shi daga majalisar Shugaban kasa shine N27,000 ga dukkanin ma’aikatan tarayyar Najeriya."

Ya kuma bayyana cewa wannan matsaya na gwamnati ba zai hana ma’aikata samun fiye da hakan daga ma’aikatansu ba, ya danganta da karfin aljihun wanda ya dauki mutum aiki.

KU KARANTA KUMA: Hako man fetur: Jihar Bauchi na gab da zama tamkar jihohin Niger Delta

A baya mun ji cewa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu cewa duba ga halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, N30,000 da ake neman a amince da shi a matsayin mafi karancin albashi ba zai ishi ma’aikacin Najeriya ba ma.

Dogara ya bayyana hakan yayinda yake karanto jawabin barka da zuwa a kwamitn wucin-gadi da aka kafa kan mafi karancin albashi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel