Zaben Ekiti: Kotu ta kunyata Fayose, ta tabbatar da nasarar gwamna Fayemi

Zaben Ekiti: Kotu ta kunyata Fayose, ta tabbatar da nasarar gwamna Fayemi

Kotun sauraron korafe korafen da suka biyo bayan zaben gwamnan jahar Ekiti daya gudana a ranar Asabar, 14 ga watan Yulin shekarar 2018, ta tabbatar da nasarar da gwamnan jahar Mista Kayode Fayemi ya samu a zaben.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu ne kotun dake zamanta a babbar birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci, inda ta fatattaki karar da dan abokin takarar gwamnan daga jam’iyyar PDP, Olusola Eleka ya shigar gabanta.

KU KARANTA; Lamari ya girmama: Dan takarar gwamnan APC ya garzaya wajen Dahiru Bauchi neman tabarraki

Tun farkon bayan kammala zaben gwamnan ne Olusola Eleka ya shigar da kara gaban kotun, inda yake zargin an gudanar da magudi a zaben, tare da ba daidai ba a yayin zaben, don haka ya nemi kotu ta sanar da shi a matsayin halastaccen gwamnan jahar Ekiti.

Sai dai bayan dogon zama tana sauraron dukkanin bangarorin dake cikin shari’ar, a yau kotun ta yanke hukuncin cewa gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi ne halastaccen gwamnan jahar saboda ya ci zabe ba tare da magudi ba, sa’annan ta fatattaki karar Eleka.

Shi dai Eleka ya kasance mataimakin gwamnan jahar Ekiti a zamanin mulkin tsohon gwamnan jahar Ayodele Fayose, wanda ake ganin shine ya daure masa gindin fitowa takarar gwamnan jahar, matakin da masana siyasar jahar ke ganin an dauka ne domin kare Fayose daga tuhume tuhume a gaba.

Idan za’a tuna hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da tsohon minista kuma tsohon gwamna Kayode Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben ne bayan ya samu kuri’u 197,462 tare da lashe kananan hukumomi 12 cikin 16 na jahar, fiye da kuri’un da PDP ta samu 177,927.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel