Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

- Jam'iyyar APC reshen jihar Filato ta nada tsohon gwamna Joshua Dariye a matsayin dan kwamitin kamfen din Gwamna Simon Lalong

- A halin yanzu dai Dariye yana can garkame a kurkuku amma hakan bai hana jam'iyyar ta bashi wannan mukamin ba

- Da ya ke tabbatar da nadin, Kwamishinan yada labarai na jihar, Yakubu Dati ya ce babu wani laifi cikin hakan

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta bawa tsohon Gwamna Joshua Dariye na jihar Filato da ke daure a gidan yari mukami a cikin Majalisar Yakin neman zaben Gwamna Simon Lalong na jihar Filato da ke son yin tazarce.

Dariye dai yana daure ne a gidan yari na Kuje da babban birnin tarayya Abuja inda ya ke zaman kaso na daurin shekaru 10.

Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Sanarwar nadin da aka yiwa Dariye ta fito ne daga bakin Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Yakubu Dati inda ya ce Dariye na cikin kwamitin yakin neman zaben Lalong.

Amma wani abin mamaki shine ba san irin rawar da Dariye zai taka ba a yakin neman zaben duba da cewa yana daure a gidan yari a Abuja.

Mai magana da yawun Gwamna Lalong ya shaidawa Premium Times cewa ba wani matsala bane don a bawa Dariye mukami a cikin kwamitin yakin neman zaben gwamnan.

"A halin yanzu Dariye ya daukaka kara, akwai yiwuwar kotu ta wanke shi kuma ya fito ya cigaba da yakin neman zabensa," a cewar mai magana da yawun gwamnan, Mark Longyn.

Longyn ya kara da cewa Dariye mutum na mai farin jini sosai da ko bai fito daga gidan yari ba zai iya gudanar da yakin neman zabe kuma ya ci zaben.

Ya bayar da misalin wasu 'yan siyasa a Najeriya da su kayi yakin neman zabe daga kurkuku kuma suka lashe zaben kamar Sanata Omisore Iyiola da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel