Badakalar Onnoghen: Yadda Buhari ya warware kullalliyar tuggun da PDP ke kullawa

Badakalar Onnoghen: Yadda Buhari ya warware kullalliyar tuggun da PDP ke kullawa

Jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC ta bayyana mamaki da yadda jam’iyyar adawa ta PDP ta kidime game da sallamar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ma tsohon Alkalin Alkalai, Mai sharia Walter Onnoghen, inda tace ina ruwan biri da gada?

Legit.ng ta ruwaito APC ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu, inda take tambayar menene dalilin da yasa PDP da dan takararta Atiku Abubakar suka shiga damuwa da cire Onnoghen, “Ko dai da walakin goro a miya ne?” Inji ta.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotun da’ar ma’aikata ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

Badakalar Onnoghen: Yadda Buhari ya warware kullalliyar tuggun da PDP ke kullawa

Buhari Onnoghen
Source: Twitter

APC ta yi gaban kanta wajen gano wasu dalilai da suka sanya take ganin jam’iyyar PDP ta kidimene kawai saboda an shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lalata musu shirin da suka kulla da Onnoghen domin kwace zaben 2019 a gaban kotu.

"Kowa na sane da alakar gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike da Onnoghen, wannan na daga cikin kulle kullen da suke yi a shirinsu na kwace zaben 2019 a gaban kotu, a yanzu abin ya bayyana karara cewa wannan ne manufar PDP, don haka suka shiga tashin hankali ganin cewa lissafi ya kwace musu.

“Sunyi nufin kwace zaben ne ta hanyar sayan shari’ar daga Alkalan da zasu saurari shari’ar bayan zabe har zuwa gaban kotun koli, kotun Allah Ya isa, wanda take a karkashin jagorancin Alkalin Alkalai Walter Onnghen, dama can haka suke yi a shekaru 16 da suka kwashe suna mulkan Najeriya.

“Wannan badakala wacce suke shiryawa, kuma Buhari ya gano, itace ta rikita dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, sakamakon asirinsu ya tonu, saboda ya san ba zai samu nasara a zaben 2019 ba.” Inji APC.

APC ta jaddada nasarar da ta samu a zaben 2015, inda tace hakan ya tabbata duk kuwa da cewa itace jam’iyyar adawa, don haka ba za ta murde zaben 2019 kawai don tana kan mulki ba, daga karshe ta gargadi kasashen Amurka, Birtaniya dasu kauce ma yi ma Najeriya katsalandan a harkokinta.

A wani labarin kuma, Akalin kotun da'ar ma'aikata, CCB, Mai sharia Danladi Umar ya dage cigaba da sauraron karar da aka shigar da tsohon Alkalin Alkalai, Mai sharia Walter Onnghen har sai 'Baba ta ji'

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel