Yanzu Yanzu: N30,000 yayi kankanta a natsayi mafi karancin albashi – Dogara

Yanzu Yanzu: N30,000 yayi kankanta a natsayi mafi karancin albashi – Dogara

- Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa N30,000 da ake neman a amince da shi a matsayin mafi karancin albashi yayi kadan da zai ishi ma'akaci

- Dogara yace hanya guda da za a bi domin magance cin hanci da rasahawa shine biyan albashin da zai wadatar da ma’aikaci amma ba wai karancin albashi ba

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu cewa duba ga halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, N30,000 da ake neman a amince da shi a matsayin mafi karancin albashi ba zai ishi ma’aikacin Najeriya ba ma.

Dogara ya bayyana hakan yayinda yake karanto jawabin barka da zuwa a kwamitn wucin-gadi da aka kafa kan mafi karancin albashi.

Yanzu Yanzu: N30,000 yayi kankanta a natsayi mafi karancin albashi – Dogara

Yanzu Yanzu: N30,000 yayi kankanta a natsayi mafi karancin albashi – Dogara
Source: Depositphotos

Yace: “hanya daya da za a magance cin hanci da rashawa shine biyan albashin da zai wadatar da ma’aikaci amma ba wai karancin albashi ba.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zanga-zanga ya barke a sakatariyar NBA kan dakatar da Onnoghen

A baya mun ji cewa mista Chris Ngige, ministan kwadago da daukar aiki ya ce karin mafi karancin albashi na ma'aikatan kasar daga N18,000 zuwa N27,000 ya kai makura wajen cancanta, amma cikin adalci na gwamnatin tarayya, ta ce zata rinka biyan ma'aikatan gwamnatin tarayya N30,000 a matsayin mafi karancin albashinsu.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Iliya Rhoda, mataimakin dartan watsa labarai na ma'aikatar da ke Abuja, wacce aka rabawa manema labarai a safiyar ranar Asabar.

A cewar ministan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai nazari kan karin mafi karancin albashi a cikin watan Nuwamba 2017, inda kuma daga karshe kwamitin ya gabatar da rahotonsa da kuma bukatunsa gaban shugaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel