Da dumi-dumi: An shiga ganawar sirri tsakanin Buhari da babban Rabaran Mbaka

Da dumi-dumi: An shiga ganawar sirri tsakanin Buhari da babban Rabaran Mbaka

A yau, Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin fittacen malamin addinin kiristan nan na darikar Kotolika, Fada Ejike Mbaka a ofishinsa da ke fadar Aso Rock a Abuja.

Malamin addinin wanda ya yi kaurin suna saboda bayyana ra'ayoyinsa a kan harkokin siyasar Najeriya ya isa ofishin shugaban kasar ne misalin karfe 12 na rana kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mr Mbaka yana daga cikin wadanda suka bayyana goyon bayansu da Shugaba Buhari a zaben 2015.

Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa babban malamin addini, Mbaka

Yanzu-yanzu: Buhari yana ganawa babban malamin addini, Mbaka
Source: UGC

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

A cikin 'yan kwanakin nan, an haska Mbaka a faifan bidiyo inda ya ke gargadin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi a kan abinda ka iya biyo baya idan bayar da tallafi ga cocinsa.

Da isarsa, ya wuce harabar ofishin shugaban kasa kuma yana ciki har zuwa lokacin da ke rubuta wannan rahoton.

Wasu na ganin wannan ziyarar na nufin zai marawa shugaba Muhammadu Buhari baya ne a zaben 2019 duba da cewa haduwarsa da Peter Obi na jam'iyyar PDP ba tayi armashi ba.

Ku biyo mu domin samun karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel