Da dumi dumi: Kotun da’ar ma’aikata ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

Da dumi dumi: Kotun da’ar ma’aikata ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

Rahoton da muke samu a yanzu ya bayyana cewa kotun da’ar ma’aikata, CCB, dake karkashin Mai sharia Danlada Umar ta dage cigaba da sauraron karar da aka shigar da tsohon Alkalin Alkalai,Walter Onnghnena gabanta har sai ‘Baba ta ji’ kamar yadda hausawa ke cewa.

Legit.ng ta ruwaito an gurfanar da mai sharia Onnoghen a gaban kotun CCB ne bayan an bankado wasu asusun bankinsa dake makare da kudaden kasashen waje da bai bayyanasu cikin kadarorinsa ba, don haka ake tuhumarsa da tafka laifuka shida.

KU KARANTA: Wani jigon jam’iyyar APC ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a Abuja

Da dumi dumi: Kotun da’ar ma’aikata ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

Buhari da Onnghen
Source: Twitter

A zaman kotun ta yau Litinin, 28 ga watan Janairu, lauyan gwamnati dake shigar da kara, Musa Ibrahim ya tuna ma kotun cewa ita da kanta ta dage shari’ar a satin data gabata zuwa yau don jin korafin bangaren wanda ake kara.

Sai dai Lauya Musa yace amma duba da cewa wasu lauyoyi sun daukaka kara a gaban kotun daukaka kara, yana neman kotun CCB ta dage cigaba da sauraron wannan kara har sai kotun daukaka ta yanke hukunci akan lamarin dake gabanta.

Nan da nan lauyan wanda ake kara, Kanu Agabi yayi wuf ya bayyana ma Alkali Danladi Umar cewa bangaren wanda ake kara basu da matsala da bukatar da lauyan masu shigar da kara ya nema, suna goyon bayan haka.

Jin haka yasa Alkali Danladi yace “Kun bukatar mu dage sauraron karar ne na tsawon yan makonnin da ake sa ran kotun daukaka kara zata yanke hukunci sai mu dawo mu cigaba da zamanmu anan ne?”

Anan ma lauyan wanda ake kara, Kanu Agabi yayi wuf ya amsa ma Alkalin cewa suna bukatar a dage sauraron karar ne har abada, daga nan sai Alkali Danladi Umar ya yanke hukuncin dage karar har sai baba ta ji, amma fa zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel