Nasarar Buhari itace za ta zama jana'izar Obasanjo a siyasa - Farfesa Sagay

Nasarar Buhari itace za ta zama jana'izar Obasanjo a siyasa - Farfesa Sagay

- Shugaban PACAC, Farfesa Itsey Sagay ya yiwa tsohon Shugaban kasa Obasanjo kaca-kace a kan katsalandan da ya ke yiwa Shugaba Buhari

- Itsey Sagay ya ce tsohon shugaban kasa Obasanjo ba shi da wasu magoya baya sai dai kokarin tayar da zaune tsaye

- Farfesa Sagay ya ce ya yi imanin Buhari zaiyi nasara a 2019 kuma wannan nasarar za ta zama mutuwar Obasanjo a siyasance

Shugaban kwamitin da ke bawa shugaba Buhari shawara kan yaki da rashawa (PACAC), Farfesa Itsey Sagay (SAN), ya yi tsokaci a kan batutuwan da ke faruwa a Najeriya musamman dakatar da alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da kuma katsalandan da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke yiwa Buhari.

Nasarar Buhari itace za ta zama jana'izar Buhari a siyasa - Farfesa Sagay

Nasarar Buhari itace za ta zama jana'izar Buhari a siyasa - Farfesa Sagay
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Sagay ya nuna goyon bayansa dari bisa dari game da dakatar da Onnoghen da Buhari ya yi bisa umurnin kotun da'ar ma'aikata CCT saboda tuhumarsa da akeyi da saba wasu dokokin aiki da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa.

Kazalika, babban lauyan ya ce baya tantama shugaba Buhari ne zai lashe zabe saboda shi talakawa suke kauna kuma nasararsa za ta zama tamkar mutuwar Obasanjo ne a siyasance kamar yadda ya fadi a wani hira da ya yi da jaridar Independent.

An tambaye shi ra'ayinsa ne game da yadda a baya Obasanjo ya ce Allah ba zai yafe masa ba idan ya marawa Atiku Abubakar baya amma kwatsam yanzu sai gashi ya yafe masa har ma kamfen ya ke masa.

Sagay ya bayar da amsa kamar haka: "Allah bai yafe ma Obasanjo, wannan soke burutsun da ya ke yi yanzu duk alamar tsinuwar Allah ce. Allah yana hukunta shi ne saboda rantsuwar da ya yi ne cewa ba zai goyi bayan Atiku ba amma kwatsam ya karya rantsuwar.

"Naji labarin yana shirin zuwa kasashen waje domin yiwa Atiku kamfen, ina fatan za su zo suyi zabe a ranar 16 ga watan Fabrairu. Suna rudan kansu ne kawai. Yanzu Obasanjo ba shi da wasu magoya baya a Najeriya.

"Buhari ya lashe zabe a shekarar 2015 ne saboda al'umma na sonsa. Babu hannun Obasanjo a ciki. Nayi farin ciki saboda a wannan karon Obasanjo ya yi hannun riga da Buhari kuma hakan zai sanya ya kara samun kuri'u fiye da 2015 kuma wannan nasarar za ta zama jana'izar Obasanjo a siyasance."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel