Abacha malamin Buhari ne, kuma shugaban kasar ya karantu da kyau – Atiku

Abacha malamin Buhari ne, kuma shugaban kasar ya karantu da kyau – Atiku

- Dan takarar shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa kusancin Abacha da Buhari ne ya sa ya ke taka kowa

- Ya ce tabbass Buhari ya karantu sosai a wajen malamin nasa

- Hakan martani ne ga tsige shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da shugaban kasar yayi

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar ya bayyana cewa kusancin Abacha da Shugaban kasa Muhmmadu Buhari ne ya sa ya ke taka kowa ya yi abinda ya ga dama ba tare da ya bi dokar wajen yanke hukunci a abubuwan da ya shafi kasar.

“Idan za a tuna a zamanin shugabancin Abacha ya tsige sarkin Musulmi da rana tsaka kuma sanin kowa ne cewa Buhari dan gaban goshin sa ne suna tare ya aikata hakan. Ka ga ko ai ya karantu sosai da yadda ake karya doka daga wajen malamin sa Abacha.” Inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa abinda da yafi tada masa hankali shine yadda kiri-kiri shugaba Buhari ya taka doka sannan yayi rugu-rugu da ita don ya cimma burin sa.

Abacha malamin Buhari ne, kuma shugaban kasar ya karantu da kyau – Atiku

Abacha malamin Buhari ne, kuma shugaban kasar ya karantu da kyau – Atiku
Source: Depositphotos

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ce ba yana sukar Buhari don yana mara wa Walter Onnoghen baya bane. “Dole mu fito mu fadi gaskiya a inda aka saba wa dokar kasa sannan mu fadi gaskiya komai dacin ta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Farawa da iyawa, Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli

“Idan sun afka wa shugabannin majalisar kasa, mun yi shiru saboda mu ba wakilai bane a majalisa, suka kai wa gidajen jaridun kasa hare-hare muka tsuke baki saboda mu ba ‘yan jarida bane, suka fada wa bangaren shari’a muka yi shiru wata rana zasu afko mana babu wanda zai cece mu."

A halin da ake ciki, mun samu labarin cewa mambobin kungiyar kare hakkin kasa da lauyoyin kungiyar kare damokradiyya sun mamaye mashigin sakatariyar kungiyar lauyoyin Najeriya a kan dakatar da Onnoghen.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masu zanga-zangan a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu sun yi kira ga Shugaban kasa da ya janye hukuncinsa sannan ya dawo da Onnoghen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel