Yanzu Yanzu: Zanga-zanga ya barke a sakatariyar NBA kan dakatar da Onnoghen

Yanzu Yanzu: Zanga-zanga ya barke a sakatariyar NBA kan dakatar da Onnoghen

- Mambobin kungiyar kare hakkin kasa da lauyoyin kungiyar kare damokradiyya sun mamaye mashigin sakatariyar kungiyar lauyoyin Najeriya kan dakatar da Onnoghen

- Magoya bayan Shugaban kasar sun ce matakin da Buhari ya dauka shine daidai domin kare martabar kasar

- Masu adawa da Buhari sun yi kira ga Shugaban kasa da ya janye hukuncinsa sannan ya dawo da Onnoghen

An gudanar da wani zanga-zanga tsakanin magoya bayan Shugaban kasa Muhaammadu Buhari da masu adawa da shi kan dakatar da Shugaban alkalan kasar, Justice Walter Onnoghen.

Magoya bayan Shugaban kasar sun ce matakin da Buhari ya dauka shine daidai domin kare martabar kasar.

A nasu bangaren, Mambobin kungiyar kare hakkin kasa da lauyoyin kungiyar kare damokradiyya sun mamaye mashigin sakatariyar kungiyar lauyoyin Najeriya.

Shugabannnan kasa Muhammadu Buhari ya tsige Onnoghen sannan ya rantsar da Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin Shugaban kungiyar alkaln Najeriya a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masu zanga-zangan a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu sun yi kira ga Shugaban kasa da ya janye hukuncinsa sannan ya dawo da Onnoghen.

Yanzu Yanzu: Zanga-zanga ya barke a sakatariyar NBA kan dakatar da Onnoghen

Yanzu Yanzu: Zanga-zanga ya barke a sakatariyar NBA kan dakatar da Onnoghen
Source: Twitter

Masu zanga-zangan sun dauki kwalayen sanarwa da rubutu daban-daban, kamar su, “Tanko Mohammed ka daina gurfanar da kanka a matsayin Shugaban alkalan Naeriya; “Ya zama dole NBA ta dauki mataki a yanzu ta hanyar umurtan lauyoyi da su ajiye kayayyakinsu,“Amaechi, El-Rufai, Akpabio, Malami, APC: Sune suka shiyar wa Onnoghen munakisa,” “Ya zama dole NC ta tafi hutu yanzu sannan ta dakatar da ustis Mohmmed,” da dai sauransu.

KU KARANTA KUMA: Da dumi dumi: Kotun da’ar ma’aikata ta dage sauraron karar Alkalin Alkalai har sai ‘Baba ta ji’

A halin da ake ciki, Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na shirin gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja a yau, Litinin, 28 ga watan Janairu kan dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata majiya na kusa da babbar jam’iyyar adawar ta ruwaito cewa za a yi zanga-zangan ne domin janyo hankalin duniya kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ke gudanar da kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel