Yanzu-yanzu: Farawa da iyawa, Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli

Yanzu-yanzu: Farawa da iyawa, Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli

Farawa da iyawa, sabon mukaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Mohammed, ya jagoranci zaman kotun koli dake birnin tarayya Abuja tare sauran abokan aikin biyar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Tanko a ranan Juma'a, 25 ga watan Junairu bayan sallamar shugaban Alkalan, Walter Onnoghen, bisa ga zargin boye wasu dukiyoyi da ya mallaka.

Sauran mambobin kotun kolin dake halarce sune Jastis Amiru Sanusi, Jastis Kudirat Kekere-Ekun, Jastis Mary Peter Odili da Jastis Paul Galinje.

Yanzu-yanzu: Farawa da iyawa, Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli

Yanzu-yanzu: Farawa da iyawa, Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli
Source: Twitter

Da safiyar yau, Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun dira ofishin shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, da safiyar Litinin bayan shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar ranan Juma'a. Majiya ta bayyanawa manema labarai.

Cikin yunkurin hanashi shiga ofishin, jami'an yan sandan sun fittitiki dukkan ma'aikatan ofishi Onoghen kuma suka buga kwado tun misalin karfe 7 na safe.

Mun kawo muku cewa Majalisar shari'a ta kasa NJC ta kira wani muhimmin taron gaggawa domin tattaunawa akan korar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa mai shari'a Walter Onnoghen daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa CJN.

Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana ne ba tare da Walter Onnoghen da mukaddashi Jastis Tanko Mohammmad ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel