Yanzu Yanzu: PDP za ta yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka kan dakatar da Onnoghen

Yanzu Yanzu: PDP za ta yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka kan dakatar da Onnoghen

- Shugabannin jam’iyyar PDP na shirin gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja

- Za su gudanar da zanga-zangan ne akan dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen

- Za kuma su janyo hankalin duniya kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ke gudanar da kasar

Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na shirin gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja a yau, Litinin, 28 ga watan Janairu kan dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

Yanzu Yanzu: PDP za ta yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka kan dakatar da Onnoghen

Yanzu Yanzu: PDP za ta yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka kan dakatar da Onnoghen
Source: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata majiya na kusa da babbar jam’iyyar adawar ta ruwaito cewa za a yi zanga-zangan ne domin janyo hankalin “duniya kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ke gudanar da kasar."

Ana kuma sanya ran za su sanar wa da jakadan batun “rashin mutunta dokar da shugaban kasar ke yi,” cewar majiyar.

A halin da ake ciki, mun ji cewa sabon mukaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Mohammed, ya jagoranci zaman kotun koli dake birnin tarayya Abuja tare sauran abokan aikin biyar.

KU KARANTA KUMA: 2019 UTME: JAMB ta tara N1.2bn cikin mako guda kacal, ta dakatar da cibiyoyi 9

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Tanko a ranan Juma'a, 25 ga watan Junairu bayan sallamar shugaban Alkalan, Walter Onnoghen, bisa ga zargin boye wasu dukiyoyi da ya mallaka.

Sauran mambobin kotun kolin dake halarce sune Jastis Amiru Sanusi, Jastis Kudirat Kekere-Ekun, Jastis Mary Peter Odili da Jastis Paul Galinje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel