Babban Faston Katolika na Yola yayi Allah-wadai da irin dabi’ar Mbaka

Babban Faston Katolika na Yola yayi Allah-wadai da irin dabi’ar Mbaka

Mun ji labari cewa babban Limamin darikar Katolika masu bin addinin Kirista a Garin Yola a cikin jihar Adamawa watau Rabaren Stephen Mamza ya caccaki wasu malaman da ke kasar nan da barin aikin Allah.

Babban Faston Katolika na Yola yayi Allah-wadai da irin dabi’ar Mbaka

Ejike Mbaka yana cikin Malamai ke shiga cikin harkar siyasa
Source: Depositphotos

Babban Shehi Stephen Mamza yayi hira da Jaridar Punch inda ya tabo batun zaben bana da kuma yadda wasu Malamai ke kutsa kai cikin siyasa. Rabaren Mamza yace kwadayi ne yake sa Malamai su na shiga wajen ‘yan siyasan kasar.

Shehin yace sam bai dace Malaman addini su rika bari ‘yan siyasa na amfani da su ba. Limamin yace ya kamata ace Malaman addini su zama masu yi wa masu mulki wa’azi ne, amma sais u ka kare da yin abin kunya saboda kwadayi.

KU KARANTA: CJN: Ana neman Majalisa ta karbe shugabanci daga hannun Buhari

Da aka tambayi Stephen Mamza game da Rabaren Ejike Mbaka wanda yake cikin darikar Katolika kuma yayi kaurin-suna, Limamin na Garin Yola yayi tir da halin Takwaran na sa wanda yace ya jawowa cocin na su abin kunya ainun.

Rabaren Stephen Mamza yake cewa ya kamata a ce an hukunta Ejike Mbaka saboda irin tsoma kan sa da yake yi cikin harkar siyasa. Limamin yace ya kamata manyan su ja-kunnen Mbaka domin lamarin sa ya fara wuce gona da iri.

Babban Limamin da Mabiya darikar Katolika da ke Adamawa yana cikin masu sukar gwamnatin Buhari wanda a cewar sa shugaban kasar ya raba kan al’umma idan aka duba yadda yake raba mukamai ba tare da yi wa kowa adalci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel