Ni zan jagoranci tantance sakamakon zaben 2019 - Yakubu

Ni zan jagoranci tantance sakamakon zaben 2019 - Yakubu

A yayin yunkuri da fafutikar tabbatar da gaskiya gami da adalci yayin babban zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe, shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi karin haske kan mataki na daurin damarar sa.

Ni zan jagoranci tantance sakamakon zaben 2019 - Yakubu

Ni zan jagoranci tantance sakamakon zaben 2019 - Yakubu
Source: Depositphotos

Domin tabbatar da tsarki na gaskiya da kuma adalci, Farfesa Yakubu ba tare da wani abokin tarayya ba, ya sha alwashin jagorantar cibiyar kidaya kuri'u da tantance sakamakon zabe a karan kansa domin sauke nauyin da rataya a wuyan sa.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana damuwa gami da fargaba ta yunkurin wasu miyagun ‘yan siyasa ma su nufin tayar da zaune tsaye, inda yayi kira ga hukumomin tsaro da su farga wajen kare martabar zaben kasa ta hanyar tsayuwar daka da sauke nauyi da ya rataya a wuyan su bisa tanadi da kuma tsare-tsare na hukumar zabe ta kasa.

Kamar yadda shafin jaridar This Day ya ruwaito, shirye-shiryen hukumar na zuwa ne biyo bayan shawararta ta bayar da dama ga ‘yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu na nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare da su kasance cikin harabar cibiyar kidaya kuri'u yayin tantance sakamakon zabe a babban ofishin ta da ke garin Abuja.

Jaridar Legit.ng ta fahimci, cibiyar kidaya kuri'u ta kasance harabar tattara dukkanin sakamakon zaben shugaban kasa da za a gudanar cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan gabanin bayyana sakamakon zaben.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane 7 a jihar Zamfara

Babban jami'in hukumar ya kuma janyo hankalin al'ummar Najeriya da kuma na kasashen ketare akan kada su sanya wata fargaba ko shakku akan nagarta da ingancin hukumar wajen tabbatar da tsarkakken zabe.

Da ya ke kira kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, Farfesa Yakubu ya kuma yi gargadin cewa dimokuradiya ba za ta ci gaba da tabbatuwa a fadin kasar nan ba matukar shugabannin da mabiya ba sa yiwa dokoki da'a da biyayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel