2019 UTME: JAMB ta tara N1.2bn cikin mako guda kacal, ta dakatar da cibiyoyi 9

2019 UTME: JAMB ta tara N1.2bn cikin mako guda kacal, ta dakatar da cibiyoyi 9

- Hukumar JAMB ta sanar da cewa ta hada kimanin naira biliyan 1.3 tsakanin ranar 18 da 24 ga watan Janairu a matsayin kudaden shiga

- Kudaden na daga ckin kudaden shiga na jarrabawa wanda aka hada ta hanyar rijistan jarrabawa ta UTME da sauransu

- Hukumar jarrabawar ta dakatar da tara daga cikin cibiyoyin jarrabawarta

Hukumar jarrabawar shiga jami’a JAMB ta sanar da cewa ta hada kimanin naira biliyan 1.3 tsakanin ranar 18 da 24 ga watan Janairu a matsayin kudaden shiga.

Makudan kudaden na daga ckin kudaden shiga na jarrabawa wanda aka hada ta hanyar rijistan jarrabawa ta UTME da sauransu.

2019 UTME: JAMB ta tara N1.2bn cikin mako guda kacal, ta dakatar da cibiyoyi 9

2019 UTME: JAMB ta tara N1.2bn cikin mako guda kacal, ta dakatar da cibiyoyi 9
Source: Depositphotos

Hakan ya kasance ne yayinda hukumar jarrabawar ta dakatar da tara daga cikin cibiyoyin jarrabawarta na kwamfuta a lokacin da ake ci gaba da yin rijista akan zargin gudanar da wasu ayyuka da suka saba doka.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta

Cibiyoyin da abun ya shafa sune: University of Benin ICT Computer Based Test (CBT) da DA Civic Centre, dukkansu a garin Benin, jihar Edo; Mardakem Company Ltd., Oron, hr Akwa Ibom; Bintels Global Services LTD, Aguleri, da kuma Noble & Shuaib ICT Ltd, Alor, jihar Anambra, da sauransu.

A cewar hukumar, a nazarn karshen mako, JAMB ta samu N42,457,657 daga amfani da kayayyakin na’urarta; N1,212,800,000 daga rijistan UTME, N13,378,604 a matsayin chaji daga cibiyoyin CBT da kuma N52,657,00 daga sauran bangarori.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel