Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun fitittiki ma'aikatan Walter Onnoghen, sun kulle ofishinsa

Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun fitittiki ma'aikatan Walter Onnoghen, sun kulle ofishinsa

Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun dira ofishin shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, da safiyar Litinin bayan shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar ranan Juma'a. Majiya ta bayyanawa manema labarai.

Cikin yunkurin hanashi shiga ofishin, jami'an yan sandan sun fittitiki dukkan ma'aikatan ofishi Onoghen kuma suka buga kwado tun misalin karfe 7 na safe.

Daya daga cikin majiyan yace, "Jami'an yan sanda sun kulle ofishin CJN. hafsoshin yan sandan sun shiga ofishoshin ma'aikatan misalin karfe 7 na safe kuma suka umurci kowa da kowa su fita daga ofishin. Daga bisani suka kulle ko ina."

Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun fitittiki ma'aikatan Walter Onnoghen, sun kulle ofishinsa

Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun fitittiki ma'aikatan Walter Onnoghen, sun kulle ofishinsa
Source: UGC

KU KARANTA:

Wannan abu ya biyo bayan sanarwan da majalisar shari'a NJC tayi na kiran ganawar gaggawa ranan Litinin domin tattaunawa kan al'amarin dakatad da Onnoghen.

Mun kawo muku rahoton cewa majalisar shari'a ta kasa NJC ta kira wani muhimmin taron gaggawa domin tattaunawa akan korar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa mai shari'a Walter Onnoghen daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa CJN.

Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana ne a ranar Litinin, da misalin karfe 10 na safe, a babban birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel