Mafi yawan sukar da Buhari ke sha daga coci ne – Fadar shugaban kasa

Mafi yawan sukar da Buhari ke sha daga coci ne – Fadar shugaban kasa

- Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina yace mafi yawan sukar da Buhari ke sha daga coci ne

- Adesina ya kalubalanci kiristoci da su dunga yi wa shugabanninsu addu'a tare da basu goyon baya maimakon korafi

- Ya fadi hakan ne a wani taro da kungiyar manema labarai na kiristocin Najeriya suka shirya

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina yace mafi akasarin korafe-korafe da yake ji akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari daga coci yake fitowa.

Adesina yayi magana a jihar Lagas a karshen mako yayin wani taro da kungiyar manema labarai na kiristocin Najeriya suka shirya.

Mafi yawan sukar da Buhari ke sha daga coci ne – Fadar shugaban kasa

Mafi yawan sukar da Buhari ke sha daga coci ne – Fadar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Adesina ya yi kira ga kiristoci da su yiwa shugabanninsu addu’a, inda yayi tambaya “Sau nawa kuke yi wa shugabanninku addu’a kuma wani irin goyon baya kuke basu? Maimakon sukar mutane a gwamnati da yi masu alkalanci, kuyi masu addu’a.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta

“Kafin karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, marigayi Ocholi ya mutu, muna da tarin kiristoci fiye da Musulmai a majalisar sannan kuma bayan mutuwarsa sai muka zama saidai... amma abun mamaki suka da dama da nake ji kan gwamnatin nan daga coci ne,” inji shi.

Adesina ya bukaci kiristoci a gwamnati da su kasance wadanda za a yi koyi da su “Ku bari walkiyarku ta haska saboda mutane su ga kyawawan ayyukanku, aka injila yace. Don haka aiki tare da gwamnati ya taimaka maku wajen taimakawa bayin Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel