Dole ka ba Alkalin Alkalai Onnoghen hakuri – Mutanen Kudu sun fadawa Buhari

Dole ka ba Alkalin Alkalai Onnoghen hakuri – Mutanen Kudu sun fadawa Buhari

- Dattawan Jihar Akwa Ibom sun nemi Majalisa su shiga maganar dakatar da Walter Onnoghen

- Manyan na Kudancin Najeriya sun soma kira ga Shugaban kasa Buhari ya bar karagar mulki

- Mutanen na Kudu maso Kudu sun nemi Shugaban kasa ya kuma nemi afuwa wajen Onnoghen

Dole ka ba Alkalin Alkalai Onnoghen hakuri – Mutanen Kudu sun fadawa Buhari

Manyan Kudu sun ce Buhari ya nemi gafarar Onnoghen
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa Dattawan Kudu maso kudancin Kasar nan su na neman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya Walter Onnoghen hakuri na dakatar da shi da yayi daga kan mukamin san a Alkalin Alkalai na Najeriya.

Dattawan Akwa Ibom sun soki wannan mataki da shugaban kasar ya dauka kwanan nan inda su ka nemi Buhari ya roki afuwa wurin Alkali mai shari’a Walter Nkanu Onnoghen, sannan kuma ya maida sa kan kujerar sa ya koma bakin aiki.

KU KARANTA: Jam’iyyar hamayya na neman Majalisa ta karbe shugabanci daga hannun Buhari

Manyan na kasar Akwa-Ibom sun bayyana cewa wasu Miyagu ne ke zagaye da shugaban kasar, kuma su ke ba shi mugayen shawara. Shugaban wadannan Dattawa da ke zaune a kudancin Najeriya sun nemi ‘yan majalisa su ma su sa baki.

Kakakin wannan kungiya, Sanata Anietie Okon yayi kira ga Majalisa ta shiga cikin wannan rikici na dakatar da babban Alkalin kasar. Sanata Okon yake cewa wannan danyen aiki da Buhari yayi ya sabawa dokar kasa kuma yana da illar gaske.

Okon ya nemi shugaban kasa Buhari yayi maza ya canza wannan mataki da ya dauka domin ganin dokar kasa tayi aikin ta. Okon ya kuma yi kira ga shugaban kasar ya sauka daga kan mulki a dalilin dakatar da CJN Walter Onnoghen da yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel