Dole a binciki Babachir Lawal da Oke yadda ake binciken Alkalin Alkalai – HEDA

Dole a binciki Babachir Lawal da Oke yadda ake binciken Alkalin Alkalai – HEDA

- Wata kungiya ta nemi a binciki wasu na kusa da Gwamnatin Buhari kamar yadda aka taso Walter Onnoghen a gaba

- Kungiyar HEDA ta bada kwanaki 30 rak domin a gudanar da bincike a kan Babachir Lawal da kuma Ayo Oke na NIA

Dole a binciki Babachir Lawal da Oke yadda ake binciken Alkalin Alkalai – HEDA

HEDA za ta je kotu muddin aka ki binciken tsohon SGF Babachir Lawal
Source: UGC

Kungiyar HEDA mai zaman kan-ta, tayi kira ga gwamnatin tarayya tayi maza ta fara binciken tsohon Sakataren gwamnatin tarayyar watau Babachir David Lawal da kuma tsohon shugaban hukumar NIA na kasa Ayo Oke.

HEDA ta yi barazanar maka gwamnatin Najeriya a kotu nan da kwanaki 30 idan har ba ta soma binciken Injiniya Babachir Lawal da Ayodele Oke ba. Kungiyar mai fafatukar ganin an gyara sha’anin mulki ta bayyana wannan ne jiya.

KU KARANTA: An hana kowa shiga gidan CJN Onnoghen da aka dakatar

A wata wasika da shugaban kungiyar ya aikawa Ministan shari’a na kasa, ya yabawa yadda gwamnatin Buhari ta ke binciken Walter Onnoghen wanda yanzu an dakatar da shi daga matsayin Alkalin Alkalai saboda zargin da ke kan sa.

Kungiyar tace yadda aka gurfanar da CJN Walter Onnoghen, haka ya zama dole a taso keyar Babachir Lawal da Ayodele Oke wadanda aka kora daga mukamin su a gwamnatin nan bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin su na ofis.

Shugaban kungiyar ta HEDA, Olanrewaju Suraju, ya bada wata guda ne ga Ministan shari’an Najeriya ya fara binciken wadannan mutane inda yace idan har wa’adin nan ya wuce ba a dauki mataki ba za su garzaya kotu da kan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel